Shan magungunan rage ciwo, zogi, raɗaɗi ko kumburi tsawon lokaci na iya janyo ko ta’azzara ciwon gyambon ciki, wato olsa.
Magungunan jinsin NSAIDs sun haɗa da: diclofenac, wanda ya shahara da suna “ciwo takwas”, “rage zogi da dai sauran sunaye. Sauran sun haɗa da paracetamol, feldene, iburofen, meloxicam, da dai sauransu.
Bayan amfanin waɗannan magunguna wajen rage ciwo, suna da komabaya wajen raunanawa tare da lalata majinar da ke yaɗe a cikin bangon tunbi domin bayar da kariya ga tunbi. Wannan majina tana nan yaɗe a cikin bangon tunbi domin kada abinci da sauran sinadaran narka abinci su shafi bangon tunbi kai tsaye har su yi wa tunbin lahani.
Domin kauce wa haɗarin janyo ko ta’azzara gyambon ciki daga shan magungunan rage ciwo tsawon lokaci, tuntuɓi likitan fisiyo idan kana fama da ciwukan jiki kamar ciwon baya, ciwon wuya, ciwon gwiwa da sauran ciwukan jiki da gaɓɓai. Likitan fisiyo na amfani da ƙwarewa domin magance ciwon jiki da gaɓɓai ba tare da dogaro da shan magunguna kullum ba.