• About us
  • Advertise
  • Privacy Policy
  • Contact
Monday, January 30, 2023
  • Login
Katsina City News
Advertisement
  • Home
  • News and Analysis
  • Biography
  • History
  • Photo News
  • Featured
  • Literature
  • Sashen Hausa
  • Weekly Columns
    • Allo
    • Fasahar Zamani
    • Kula da Lafiya
    • Labarun Fim
    • Rubutu da Marubuta
No Result
View All Result
  • Home
  • News and Analysis
  • Biography
  • History
  • Photo News
  • Featured
  • Literature
  • Sashen Hausa
  • Weekly Columns
    • Allo
    • Fasahar Zamani
    • Kula da Lafiya
    • Labarun Fim
    • Rubutu da Marubuta
No Result
View All Result
Katsina City News
No Result
View All Result
Home Weekly Columns Kula da Lafiya

Nawa ne nauyin jakar da ya kamata yaro ya riƙa ratayawa domin kiyaye ciwon jiki?

December 28, 2022
in Kula da Lafiya
0
Nawa ne nauyin jakar da ya kamata yaro ya riƙa ratayawa domin kiyaye ciwon jiki?
0
SHARES
12
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

©️ Physiology Hausa

Wannan amsa na nan cikin shawarwari takwas ga iyaye da malamai game da rataya jakar makaranta.

Duk da muhimmancin jakar makaranta ga ɗalibi, kulawa da lafiyarsa ma na da muhimmancin gaske. Sau da yawa, ƙorafe-ƙorafen yara ‘yan makaranta kan matsananciyar gajiya, ciwon baya, wuya ko kafaɗu na da alaƙa da ɗabi’ar nan ta rataya jakar makaranta maƙare da littafai, kayan rubutu, abinci ko abinsha, wani lokacin ma har da sauran kayayyakin da ba a buƙatarsu a makaranta.

Bugu da ƙari, bincike ya nuna yadda rataya jaka mai nauyi ke sauya lafiyar numfashi saboda yadda nauyin jakar ke takura haƙarƙari da huhu.

Haka nan, masana lafiyar ƙashin gadon baya sun ja hankalin iyaye da malamai cewa lafta wa yara jakankuna masu nauyin gaske na da gagarumar illa ga lafiyar yaran.

Shawarwari takwas domin kiyayewa:

1) A tabbatar nauyin jakar baya ba ta wuce kaso goma zuwa sha biyar cikin ɗari(10 – 15%) na nauyin yaro ba. Nauyin jakar bayan da ya wuce kaso goma zuwa sha biyar cikin ɗari(10 – 15%) na nauyin yaro zai riƙa rinjayar yaro wanda hakan kan sa yaro durƙusawa ko sunkuyawa gaba domin kar nauyin jakar ya rinjaye shi.

Misali, idan nauyin yaro ya kai kilogiram talatin (30Kg) a kan ma’aunin nauyi; to nauyin jakar da ya kamata ta ɗinga ratayawa zai yi dai-dai ne da kilogiram uku zuwa uku da rabi (3 – 3.5Kg).

2) A yayin da aka goya jakar baya, ba a son ta sauko ko ta zarce fiye da farkon ƙashin ƙugu, ko kuma sama da maɗaurin wando kaɗan.

3) A zaɓi jaka mai aljihuna; a sanya abin da ke da tsini ko kaifi a aljihu mafi nesa da gadon baya. Sannan a sanya kayan da ke da nauyi a aljihu mafi kusa da gadon baya.

4) Lafta wa yara littattafai a cikin jakar makarantarsu ba dole ba ne. Girman jakar makaranta fiye da ƙima kan sanya yara ɗaukar kayayyaki masu nauyi da ba a buƙatarsu a makaranta.

5) A umarci yaro da rataya maratayan jakar biyu a kafaɗunsa na hagu da dama kowane lokaci. Domin sanya maratayin jakar a kafaɗa ɗaya kawai zai kawo rinjayar nauyin zuwa ɓari ɗaya; wanda hakan kan kawo ciwon wuya, kafaɗa, baya da kuma tasgaɗewar ƙashin gadon baya yau da gobe.

6) A zaɓi maratayin jaka mai faɗi kuma mai taushi; domin siririn maratayin jaka na iya nitsewa cikin kafaɗa har ya ci wa yaro jiki.

7) A zaɓi jaka mai maratayan da za a iya ƙarawa ko ragewa dai-dai da tsayin yaro. Domin maratayan jakar da ba za a iya rage su ba na iya kawo zarcewar ko taruwar nauyin jakar zuwa inda ba a buƙatarsa a gadon baya.

8) Idan jakar yaro ta yi nauyi sosai, a shawarci malamansa domin rage littattafan da za a iya barin su a makaranta domin rage nauyin dakon littattafan daga gida zuwa makaranta kullum.

A yayin da yaro ya fara ƙorafin matsananciyar gajiya, ciwon baya, wuya ko kafaɗu, tuntuɓi likitan fisiyo domin neman shawarwari da kuma magance ƙorafe-ƙorafen.

Share

Related

Source: Physiology Hausa
Via: Katsina City News
Previous Post

NAN committed to workers’ welfare, to set up joint c’ttee- MD

Next Post

ƳAN BINDIGA SUN KAI HARI CIKIN GARIN BATSARI

Next Post
ƳAN BINDIGA SUN KAI HARI CIKIN GARIN BATSARI

ƳAN BINDIGA SUN KAI HARI CIKIN GARIN BATSARI

Recent Posts

  • APC ta gano kafafen yada labaran da PDP ke ɗaukar nauyi su yaɗa karya a kan Tinubu
  • Emefiele: We’ve collected N1.9trn old naira notes so far — N900bn more to go
  • Hanyoyi Shida Domin Kiyaye Basir Cikin Sauƙi.
  • Bankin CBN Ya Samar Da Naira Miliyan 120 Domin Yin Canjin Kudi A Katsina.
  • INEC ta kara tsawaita wa’adin karbar katin zabe

Recent Comments

No comments to show.

Archives

  • January 2023
  • December 2022
  • November 2022
  • October 2022
  • September 2022
  • August 2022
  • July 2022

Categories

  • Biography
  • City News
  • Condolence
  • Fasahar zamani
  • Featured
  • General Stories
  • History
  • Kula da Lafiya
  • Labaran Fim
  • Literature
  • News and Analysis
  • News and Reports
  • Photo News
  • Rubutu da Marubuta
  • Sashen Hausa
  • Tarihin Kasar Katsina

Browse by Category

  • Biography
  • City News
  • Condolence
  • Fasahar zamani
  • Featured
  • General Stories
  • History
  • Kula da Lafiya
  • Labaran Fim
  • Literature
  • News and Analysis
  • News and Reports
  • Photo News
  • Rubutu da Marubuta
  • Sashen Hausa
  • Tarihin Kasar Katsina
  • About us
  • Advertise
  • Privacy Policy
  • Contact

No Result
View All Result
  • Home
  • News and Analysis
  • Biography
  • History
  • Photo News
  • Featured
  • Literature
  • Sashen Hausa
  • Weekly Columns
    • Allo
    • Fasahar Zamani
    • Kula da Lafiya
    • Labarun Fim
    • Rubutu da Marubuta

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In