Shan ruwa kafin aci komai ƴana da matuƙar
mahimmanci ga jikin ɗan adam ta hanyar fuskoki da dama, A duk ayyukan ka na yau da kullum, jikinka na bukatar karfi. Wannan dalilin ne yasa kake shan ruwa don kashe kishi. Amma saboda wahalar yau da kullum, wasu kan manta da ruwan gaba daya. Amma shin ko kunsan cewa shan ruwa da sassafe na da matukar amfani ga lafiyar mu kuwa???
Jikinka na bukatar ruwa kana tashi da sassafe. Kana tashi tun da safe, dauki kofin ruwanka ka sha kawai, amma dan allah a tabbatar da lafiya da tsaftar ruwan kafin a sha, Akwai tabbacin cewa zaka ga sauyi a yanayin lafiyarka cikin kankanin lokaci.
Ga wasu daga cikin amfanin shan ruwa da sassafe daga tashi bacci kafin a ci komai.
- Shan ruwa da sassafe na samarwa da jikin dan Adam karin ruwa, duba da irin sa’o’in da aka dauka ana bacci.
- Shan ruwa kafin a ci abinci da safe na kara karsashi da karfin jiki.
- Shan ruwa da sassafe kafin a ci komai na tada kwakwalwa.
- Shan ruwa da sassafe kafin a ci komai na tsaftace jiki daga cutuka.
- Shan ruwa da sassafe kafin a ci abinci na yakar cutuka tare da kara garkuwa ga jikin dan Adam
- Shan ruwa da sassafe yana sa narkewar abinci kamar yadda ya dace.
- Hakazalika, yana sa a rage kiba, ga masu muguwar kiba.
- Yana gyara launin fata tare da sanya walwalin fata da walkiya.
- Yana kariya daga ciwon koda tare da tsaftace mafitsara daga kwayoyin cuta.
- Shan ruwa da safe kafin cin abinci na taimakawa tsawon gashin kai tare da walkiyarshi.
Daga RCHP: Belya Ahmad Magami.
Source:
Culled
Via:
Katsina City News