A jikin mutum akwai jijiyoyi iri-iri da suke taimakawa wajen sadarwa domin ayyukan sassan jiki su ci gaba. Jijiya na da kamanni kamar na igiya, zare, ko tsirkiya kuma tana da ɗabi’ar ɗanko, wato tana iya talewa sannan ta dawo.
A taƙaice, akwai jijiyoyi iri uku kamar haka:
- Jijiyar Tantani: jijiyar tantani, wato “tendon”, jijiya ce da ke sadar da tsoka zuwa ga ƙashi. Wato ita ce ke ɗaure tsoka a jikin ƙashi.
- Jijiyar Laka: jijiyar laka, wato “spinal nerve”, jijiya ce daga laka zuwa sassan jiki. Idan saƙonni suka sauko daga ƙwaƙwalwa za su bi ta laka ne sannan kuma su bi jijiyar laka har su isa ga sassan jiki domin kai saƙonnin ƙwaƙwalwa.
- Jijiyar jini: jijiyar jini, wato “blood vessel”, jijiya ce majinaciya da ke kaiwa ko ɗauko jini daga zuciya zuwa sassan jiki.
©Physiotherapy Hausa
Source:
Physiotherapy Hausa
Via:
Katsina City News