Tatsuniyoyi Biyar Game Da Ciwon Gwiwa
©️ Physiology Hausa
Nau’in ciwon gwiwa wanda ake cewa amosanin gwiwa, wato “knee osteoarthritis” a turance, nau’in ciwon gwiwa ne sakamakon zaizayewar gurunguntsin gaɓar gwiwa. Gurunguntsin gaɓa wani matashi ne da ke samar da taushi a gaɓa domin taimaka wa ƙashi da ƙashi yin gogayya da juna ba tare da wata tirjiya ba.
Sai dai, wannan ciwo na amosanin gwiwa na fama da gurguwar fahimta da kuma ɗumbun tatsuniyoyi da ke kewaye da shi, wanda hakan ne kan kawo tsaiko wajen ɗaukan matakan da suka kamata wajen neman hanyoyin da za a shawo kan ciwon daga tushe.
Daga cikin tatsuniyoyin da suka shafi ciwon amosanin gwiwa akwai:
- Cewa wai ciwon amosanin gwiwa ciwon sanyi ne.
Ciwon amosanin gwiwa ba shi da wata alaƙa da sanyi ko ciwon sanyi, saboda haka, ba sanyi ne ke sababinsa ba face zaizayewar gurunguntsin gaɓa. Sai dai, akwai ɓuƙatar bambancewa tsakanin ciwon amosanin gaɓa wato “osteoarthritis” da kuma ciwon sanyin ƙashi wato “rheumatoid arthritis”, wanda ciwon kumburin gaɓɓai ne da ya fi shafar ƙananun gaɓɓai kamar gaɓoɓin yatsun hannu da ƙafa.
Bugu da ƙari, kamar yadda aka ambata cewa ba sanyi ne sababin ciwon amosanin gwiwa ba, amma yanayin sanyi ko hunturu, danshi ko laima ko kuma kaɗawar iska mai sanyi na iya ta’azzara ciwon amosanin gwiwa.
- Cewa kowane tsoho sai ya samu ciwon amosanin gwiwa.
Cewa kowanne tsoho ko duk wanda shekarunsa suka miƙa tilas ne zai gamu da ciwon gwiwa tatsuniya ce kawai. Kawai dai shekaru na miƙawa haɗarin kamuwa da ciwon na ƙaruwa ne. Saboda haka sau da dama tsofi kan ƙare rayuwarsu ba tare da sun gamu da ciwon ba.
Haka nan, kowa, a kuma kowace shekara na iya samun wannnan ciwo musamman idan yana da matsalolin da ke da haɗarin janyo shi.
- Cewa shan magungunan rage ciwo shi ne kaɗai zai magance ciwon gwiwar.
Magungunan rage raɗaɗin ciwo jinsin ‘NSAIDs’ ana amfani da sune kaɗai domin rage matsanancin ciwo na wani ɗan lokaci.
Amma irin waɗannan magunguna ko kaɗan ba su da tasirin warkar da zaizayewar gurunguntsin gaɓa, sai dai rage raɗaɗin ciwon na ɗan lokaci. Kuma a yayin da aikinsu ya ƙare a jiki ciwon zai sake dawowa sabo ne.
- Cewa ciwon gwiwar ana warkewa gaba ɗaya.
Ciwon amosanin gwiwa kamar yadda muka ambata cewa yana faruwa ne sakamakon zaizayewar gurunguntsin gaɓar gwiwa. Saboda haka, zuwa yanzu babu wani magani da aka sani yana toho da gurunguntsin da ya riga ya zaizaye.
Sai dai akwai magungunan da ka iya taimakawa wajen ƙara lafiyar gurunguntsin da ya ragu, da kuma hana ci gaban zaizayewarsa.
- Cewa guje wa ayyukan da ke kawo motsa gaɓar gwiwa zai rage ta’azzarar ciwon.
Kamar yadda aka sani a yayin da ciwon ya ta’azzara masu ciwon kan guje wa ayyukan da ke da alaƙa da motsin gwiwar tsawon lokaci, kamar tafiya. Sai dai guje wa motsa gaɓar gwiwar yadda ya kamata tsawon lokaci na da gagarumar illa ga lafiyar gwiwar.
Daga ƙarshe, masu ciwon amosanin gwiwa na buƙatar ganin likitan fisiyo da zarar sun fara jin alamun ciwon domin shawo kan ciwon ta hanyar amfani da na’urorin rage ciwo da kuma keɓaɓɓen atisaye da zai taimaka wajen ƙarfafa tsokokin da ke riƙe da gwiwa — wanda hakan zai rage saurin zaizayewar gurunguntsin gaɓar gwiwa.