• About us
  • Advertise
  • Privacy Policy
  • Contact
Katsina City News
Advertisement
  • Home
  • News and Analysis
  • Biography
  • History
  • Photo News
  • Featured
  • Literature
  • Sashen Hausa
  • Weekly Columns
    • Allo
    • Fasahar Zamani
    • Kula da Lafiya
    • Labarun Fim
    • Rubutu da Marubuta
No Result
View All Result
  • Home
  • News and Analysis
  • Biography
  • History
  • Photo News
  • Featured
  • Literature
  • Sashen Hausa
  • Weekly Columns
    • Allo
    • Fasahar Zamani
    • Kula da Lafiya
    • Labarun Fim
    • Rubutu da Marubuta
No Result
View All Result
Katsina City News
No Result
View All Result
Home Weekly Columns Kula da Lafiya

Jaririn ya yi kuka? Me ye makomar rashin kukan nan-take?

Katsina City News by Katsina City News
November 10, 2022
in Kula da Lafiya
0
Jaririn ya yi kuka? Me ye makomar rashin kukan nan-take?
0
SHARES
9
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

Kukan jariri da zarar an haife shi muhimmin abin sauraro ne ga uwa, ungozoma da dangi. Kuka yana nuna cewa jariri a raye ya zo duniya. Kuma hatta a lamarin rabon gado kukan jariri abin lura ne.

Sai dai, gaza yin kuka ko kuma jinkirin kukan jariri zuwa wasu ‘yan mintina na nuni da cewa jariri bai fara numfashi nan-take ba bayan haihuwa. Saboda ba a kuka sai da numfashi. A taÆ™aice, kukan farko na jariri na nufin numfashin farko.

Idan aka lura jariri bai yi kuka ba bayan haihuwa, ungozoma ko likita na amfani da ƙwarewa domin yi wa jariri ƙaimin numfashi domin ceto rayuwa da lafiyarsa.

Ana nasarar ceto dubban jarirai daga wannan matsala, a yayin da wasu kuma ke mutuwa.

Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce, ƙiyasin jarirai 900,000 ke mutuwa duk shekara sanadiyar gaza fara numfashi bayan haihuwa. Kuma matsalar na daga cikin matsalolin da ke lashe rayukan jarirai kai tsaye.

A lokacin da jariri yake cikin uwa, yana karɓar iskar oksijin da sauran sinadaran abinci ta jijiyoyin cibiya. Ana sa ran jariri ya koma shaƙar oksijin da kansa ta hanyar numfashi da zarar ya faɗo duniya.

Saboda haka, gaza fara numfashi ga jariri bayan haihuwa na nufi da rashin oksijin ga ƙwaƙwalwa. Rashin oksijin ga ƙwaƙwalwa kuwa na da haɗarin gaske. Domin yana haifar da mummunan lahani ga ƙwaƙwalwa wace ke sarrafa sassan jiki.

Wasu sabuban da ke hana jariri fara numfashi na faruwa ne tun a cikin uwa, inda wasu kuma ke faruwa yayin naƙuɗa ko haihuwa.

Daga cikin sabuban da ke iya janyo gazawa ko jinkirin fara numfashi ga jariri sun haÉ—a da:

  1. Matsalolin jijiyoyin cibiya: Cibiya na iya fuskantar ƙullewa, shaƙewa ko kuma dannewa. Hakan kuma na nufi da katsewar oksijin ga jariri.
  2. Girman kan jariri: Idan girman kan jariri ya wuce faɗin mafitar ƙugun uwa, to ana iya samun tangarɗar naƙuda.
  3. Juyewar kwanciyar jariri a ciki: Haɗarin samun tangarɗar naƙuda na ƙaruwa da juyewar kwanciyar jariri.
  4. Mummunar zuba ko ɓallewa jini kafin ko yayin naƙuda.
  5. Toshewar hanyoyin numfashi, ko dai saboda tawayar halitta ko kuma shaƙar ruwan mahaifa.
  6. Fashewa ko ɓallewar mahaifa.
  7. Matsananciyar ƙamfar jini, da dai sauransu.

To ko mece ce makomar ƙwaƙwalwar jaririn da ya gaza yin kuka bayan haihuwa?

Kamar yadda aka ambata a baya cewa rashin oksijin ga ƙwaƙwalwa mummunan lahani ne. Saboda haka, tsawon lokacin da aka ɗauka jariri bai yi kuka ba, wato shi ne gwargwadon tsananin lahanin da ake zaton ya faru ga ƙwaƙwalwa.

Idan hakan ta faru, jariri na gamuwa da “shanyewar Æ™waÆ™walwa”, wato “cerebral palsy” a yaren likita, larura ce da ke shafar dukan sassan jiki. Daga cikin inda ta fi shafa akwai gangan jiki.

Jaririn da ya gamu da “shanyewar Æ™waÆ™walwa” yana fuskantar jinkirin matakan girma. Misali, idan lafiyayyen jariri zai iya riÆ™e wuya a wata uku zuwa huÉ—un farko, to jariri mai “shanyewar Æ™waÆ™walwa” zai yi jinkirin watanni kafin ya cimma wannan matakin girma.

Daga Æ™arshe, jariran da suka gamu da “shanyewar Æ™waÆ™walwa” sanadiyar gaza kuka bayan haihuwa na fuskantar barazanar nakasa idan ba a É—auki matakan da suka kamata tun da wuri ba.

Daga cikin matakan akwai ganin likitan fisiyo domin kiyaye nakasar sassan jiki da kuma bunƙasa aikin sassan jiki domin su cimma matakan girma kamar riƙe wuya, zama, tsaiwa da tafiya.

Aminu Abdullahi Dan’magina
Lafiya Uwar Jiki
10th, November, 2022

Share

Related

Source: Culled: Lafiya Uwar Jiki Page
Via: Katsina City News
Previous Post

Idan a ka cire tallafin man fetur sai ya koma lita É—aya N410 — NNPC

Next Post

Gwamnatin Kaduna ya ƙaryata rahoton kai hari kan titin Abuja-Kaduna

Next Post
Gwamnatin Kaduna ya ƙaryata rahoton kai hari kan titin Abuja-Kaduna

Gwamnatin Kaduna ya ƙaryata rahoton kai hari kan titin Abuja-Kaduna

Recent Posts

  • Dr. Dikko sworn in as Governor, takes over from Masari in Katsina State.
  • Tinubu Ya Nada Dele Alake A Matsayin Mai Magana Da Yawunsa
  • In inaugural address, Tinubu preaches unity, commitment to nation-building
  • Jawabin Farko a Matsayin Shugaban Æ™asa: Tinubu ya cire Tallafin Mai gaba É—aya
  • Malam Dikko Umar Radda ya zama sabon gwamnan jihar Katsina

Recent Comments

No comments to show.

Archives

  • May 2023
  • April 2023
  • March 2023
  • February 2023
  • January 2023
  • December 2022
  • November 2022
  • October 2022
  • September 2022
  • August 2022
  • July 2022

Categories

  • Biography
  • City News
  • Condolence
  • English
  • Fasahar zamani
  • Featured
  • General Stories
  • History
  • Interview
  • Kula da Lafiya
  • Labaran Fim
  • Literature
  • News and Analysis
  • News and Reports
  • Photo News
  • Press Release
  • Rubutu da Marubuta
  • Sashen Hausa
  • Sashin Hausa
  • Tarihin Kasar Katsina

Browse by Category

  • Biography
  • City News
  • Condolence
  • English
  • Fasahar zamani
  • Featured
  • General Stories
  • History
  • Interview
  • Kula da Lafiya
  • Labaran Fim
  • Literature
  • News and Analysis
  • News and Reports
  • Photo News
  • Press Release
  • Rubutu da Marubuta
  • Sashen Hausa
  • Sashin Hausa
  • Tarihin Kasar Katsina
  • About us
  • Advertise
  • Privacy Policy
  • Contact

© 2023 JNews - Premium WordPress news & magazine theme by Jegtheme.

No Result
View All Result
  • Home
  • News and Analysis
  • Biography
  • History
  • Photo News
  • Featured
  • Literature
  • Sashen Hausa
  • Weekly Columns
    • Allo
    • Fasahar Zamani
    • Kula da Lafiya
    • Labarun Fim
    • Rubutu da Marubuta

© 2023 JNews - Premium WordPress news & magazine theme by Jegtheme.