• About us
  • Advertise
  • Privacy Policy
  • Contact
Katsina City News
Advertisement
  • Home
  • News and Analysis
  • Biography
  • History
  • Photo News
  • Featured
  • Literature
  • Sashen Hausa
  • Weekly Columns
    • Allo
    • Fasahar Zamani
    • Kula da Lafiya
    • Labarun Fim
    • Rubutu da Marubuta
No Result
View All Result
  • Home
  • News and Analysis
  • Biography
  • History
  • Photo News
  • Featured
  • Literature
  • Sashen Hausa
  • Weekly Columns
    • Allo
    • Fasahar Zamani
    • Kula da Lafiya
    • Labarun Fim
    • Rubutu da Marubuta
No Result
View All Result
Katsina City News
No Result
View All Result
Home Weekly Columns Kula da Lafiya

Duba muhimman abubuwa 12 da ya kamata ka sani game da maɗiga domin ceto jarirai.

Katsina City News by Katsina City News
March 31, 2023
in Kula da Lafiya
0
Duba muhimman abubuwa 12 da ya kamata ka sani game da maɗiga domin ceto jarirai.
0
SHARES
12
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter
  1. Me faɗawa ko bullowar maɗiga ke nufi?
  2. Yaushe maɗiga ya kamata ta rufe?

Shafin Physiotherapy Hausa

  1. Bayan haihuwa, ƙashin ƙoƙon kan jarirai a rarrabe yake kuma ya ƙunshi ƙasusuwa guda biyar ne: biyu a gaba, biyu a tsakiya, sannan ɗaya a ƙeya. Maɗiga wani gurbi ne mai taushi daga gurunguntsi da tantani, saɓanin ƙashi, a mahaɗar waɗannan ƙasusuwa.

2.Hikimar kasancewar ƙashin ƙoƙon kan jarirai a rarrabe shi ne domin kan ya sami sauƙin fitowa daga ƙugun uwa yayin haihuwa. Bugu da ƙari, kasancewar ƙoƙon kan a rarrabe zai bai wa ƙwaƙwalwa damar girma kafin ƙasusuwan su haɗe.

  1. Bayan haihuwar jarirai, akwai maɗigai har guda shida a ƙoƙon kai. Sai dai, an fi lura da maɗigar tsakiyar kai, wato ta saman goshi, da kuma ta ƙeya.
  2. Maɗigar tsakiyar kai, ita ce maɗigar gaba, wato ‘anterior fontanelle’ a turancin likita. Kuma wannan maɗiga ita ce mafi girma kuma wace aka fi lura da ita cikin maɗigai shida da ke ƙoƙon kan jarirai. Sauran maɗigan biyar suna rufewa da wuri tun a makonni zuwa watannin farko na rayuwar jarirai.
  3. Maɗigar tsakiyar kai tana da kusurwa huɗu kuma tana da sifar daimon. Matsakaicin faɗinta ya kai santimita 2.1. Sai dai, akwai wasu larurori da ke janyo buɗewar maɗigar fiye da ƙima.
  4. A yayin da jariri yake cikin ƙoshin lafiya, maɗigar tsakiyar kai akasari a shafe take ko kuma ta ɗan lotsa kaɗan. Amma ana iya ganin ta ɗan ɗago sama yayin da yaro ke kuka, amai ko kuma yayin da yake kwance. Har wa yau, maɗigar tana kasancewa cikin harbawa ne a kowane lokaci kamar harbawar zuciya.
  5. To ko yaushe maɗigar tsakiyar kan ya kamata ta rufe? Maɗigar tsakiyar kai tana rufewa tsakanin watanni 13 zuwa 24 bayan haihuwa. Amma akwai larurorin da ke shafar ginin ƙasusuwan fuska da ƙoƙon kai waɗanda ke haddasa rufewar maɗigar da wuri. Haka nan, rufewar maɗigar da wuri na iya janyo dakushewar girman ƙoƙon kai da kuma ƙwaƙwalwa.
  6. Jariran da maɗigarsu ta rufe da wuri suna da haɗarin samun ƙaramin kai da kuma dakushewar aikin ƙwaƙwalwa. Hakan kuma na iya kawo jinkiri ga matakan girmansu, misali, gaza iya riƙe wuya, zama, tsaiwa ko tafiya a watannin da aka saba gani.
  7. Kamar yadda aka ambata a sama, cewa akasari maɗiga a shafe take, Sai dai ana iya ganin faɗawar maɗigar , wato ta rufta ciki, musamman idan ruwan jikin jariri ya yi ƙasa sakamakon wata larura ko kuma ƙaranci ko rashin ingancin ruwan nonon uwa ko abinci.
  8. Kamar yadda maɗiga za ta iya faɗawa ciki, haka kuma za ta iya bulli waje yayin da jariri ke fama da cutukan da ke haddasa batsewar ƙoƙon kai sakamakon wani kumburi, taruwar ruwa ko jini a cikin ƙoƙon kai.
  9. Rufewar maɗigar tsakiya kai ƙasa da watanni 13 tare da bayyanar jinkirin matakan girman yaro ko kuma bayyanar alamomi kamar jijjiga, rirriƙewar gaɓoɓi, dalalar da yawu ko gani hararagarke duk na nufin a gaggauta ganin likita.
  10. Bugu da ƙari, faɗawar maɗiga ko kumburowarta waje tare da alamomi kamar yawan kuka, zazzaɓi, shawara da sauransu duk na nufin gaggauta ganin likita.

Duba ƙarin hotuna a ‘comment section’.

Share

Related

Source: Physiotherapy Hausa
Via: Katsina City News
Previous Post

Dakata! Har yanzu ni ne gwamna – Ganduje ya faɗa wa Abba Gida-Gida

Next Post

Nigerian Media Get National Complaints Commission

Next Post
Nigerian Media Get National Complaints Commission

Nigerian Media Get National Complaints Commission

Recent Posts

  • Hajj 2023: Azman begins airlift of pilgrims Today
  • Hajj Airlift: NAHCON Airlift 14,000 pilgrims in 33 flights operations, set up back up plans
  • Hajj 2023: Plateau pilgrims “stranded’ over “failure to remit funds” for Hajj officials
  • Abin da aka tattauna a taron Tinubu da gwamnonin Jam’iyyar APC
  • Makkah service providers pledges ‘memorable’ Hajj 2023 for Nigerian pilgrims

Recent Comments

No comments to show.

Archives

  • June 2023
  • May 2023
  • April 2023
  • March 2023
  • February 2023
  • January 2023
  • December 2022
  • November 2022
  • October 2022
  • September 2022
  • August 2022
  • July 2022

Categories

  • Biography
  • City News
  • Condolence
  • English
  • Fasahar zamani
  • Featured
  • General Stories
  • History
  • Interview
  • Kula da Lafiya
  • Labaran Fim
  • Literature
  • News and Analysis
  • News and Reports
  • Photo News
  • Press Release
  • Rubutu da Marubuta
  • Sashen Hausa
  • Sashin Hausa
  • Tarihin Kasar Katsina

Browse by Category

  • Biography
  • City News
  • Condolence
  • English
  • Fasahar zamani
  • Featured
  • General Stories
  • History
  • Interview
  • Kula da Lafiya
  • Labaran Fim
  • Literature
  • News and Analysis
  • News and Reports
  • Photo News
  • Press Release
  • Rubutu da Marubuta
  • Sashen Hausa
  • Sashin Hausa
  • Tarihin Kasar Katsina
  • About us
  • Advertise
  • Privacy Policy
  • Contact

© 2023 JNews - Premium WordPress news & magazine theme by Jegtheme.

No Result
View All Result
  • Home
  • News and Analysis
  • Biography
  • History
  • Photo News
  • Featured
  • Literature
  • Sashen Hausa
  • Weekly Columns
    • Allo
    • Fasahar Zamani
    • Kula da Lafiya
    • Labarun Fim
    • Rubutu da Marubuta

© 2023 JNews - Premium WordPress news & magazine theme by Jegtheme.