Sanyin ƙanƙara na daga cikin abubuwan da ake amfani da su wajen rage raɗaɗin ciwo bayan samun raunuka kamar targaɗe, cirar nama, gocewa/gurɗewar gaɓa da sauransu.
Amafani da ƙanƙara na taimakawa ta hanyoyin biyar kamar haka:
1] Sanyin ƙanƙara na sanya jijiyoyin jini su matse, saboda haka yawan jinin da ke zagayawa a wurin raunin zai ragu.
2] Ƙanƙara na rage kumburin da ke biyo bayan rauni.
3] Ƙanƙara na rage taruwar jini ko kuma kwararar jinin zuwa kewayen raunin.
4] Ƙanƙara na rage borin tsoka, wato ‘muscle spasm’ a turance .
5] Ƙanƙara na rage saurin aikin jijiyoyin laka da ke kai saƙon jin ciwo zuwa ƙwaƙwalwa. Saboda haka zogin ciwon zai ragu.
Saboda haka, ƙanƙara na rage raɗaɗi ko zogin ciwo, musamman a raunukan da aka samu yayin motsa jiki, wasannin guje-guje da tsalle-tsalle, kamar targaɗe, cirar nama ko tsinkewar nama da sauransu.
Tabbatar akwai likitan fisiyo a ƙungiyar ƙwallon kafanka domin samun taimakon gaggawa bayan samun raunuka.
©Physiotherapy Hausa