©️ Physiology Hausa
- Ƙari wani dunƙulallen bulli ne mai ɗan taushi ko tauri da kan fito a sassan jiki. Daga cikin ire-iren ƙari da ke fitowa a sassan jiki akwai wani ƙari da ake ce masa ‘ganglion cyst’ a turance. Irin wannan ƙari yawanci yana fitowa a kan gaɓa ne.
- Girman ƙarin kan kasance kamar girman ƙwayar wake zuwa girman ƙwayar gurjiya. Yanayinsa kuwa idan aka taɓa ko aka latsa yana kama da na balan-balan ko ‘yar mitsitsiyar ƙwallo cike da ruwa mai kauri. A dunƙule dai, wannan ƙari bulli ne da ke ɗauke da wani ruwa mai yauƙi da kauri a ciki.
- Abin farin cikin shi ne wannan ƙari ba kansa /daji ba ne. Saboda haka, babu fargabar cewa zai iya fantsama zuwa sassan jiki ko kuma ya tilasta yanke hannun.
- Kaso tamanin da takwas cikin ɗari (88%) na wannan ƙari na fitowa ne kan gaɓar tsintsiyar hannu, kaso goma sha ɗaya cikin ɗari (11%) kuma yana fitowa ne a gaɓoɓin tafin sawu da idon sawu.
- Kowa zai iya samun wannan ƙari, sai dai mata sun ninka maza sau uku wajen samun ƙarin tsintsiyar hannu. Kuma kaso saba’in cikin ɗari (70%) yana faruwa ne tsakanin shekaru 20 zuwa 40 na rayuwa.
- Kaso sittin zuwa saba’in cikin ɗari (60 – 70%) na ƙarin tsintsiyar hannu yana fitowa ne a bayan tsintsiyar hannu. Inda sauran kason ke fitowa a gaban ko gefen tsintsiyar hannu.
- To ko me ke kawo wannan ƙari? Babu wani takamaiman sababi da ke kawo wannan ƙari! Sai dai ana ganin bugu, ƙaban majinar gaɓa, tunzuri ga majina ko tantanin gaɓa sakamakon ayyukan da ke buƙatar maimaituwar motsin gaɓar tsintsiyar hannu na ƙara haɗarin faruwarsa.
- Alamomin ƙarin tsintsiyar hannu: Daga cikin alamomin ƙarin tsintsiyar hannu akwai:
i. bayyanar bulli ko tudun ƙarin idan aka lanƙwashe gaɓar tsintsiyar hannu. Kuma ƙarin a wuri guda yake, ba yawo yake yi ba.
ii. ƙarin yana girma ne ƙaɗan da kaɗan, zai iya ɓullowa katsam, a wani lokaci kuma sai ya ƙanƙance ko ma ya ɓace. Haka kuma, zai iya dawowa katsam.
iii. Yawanci ƙarin tsintsiyar hannu ba ya ciwo kuma ba shi da wata matsala. Amma ya kan fara ciwo ne idan ƙarin ya fara shaƙe ko danne jijiyar laka a hanyarta ta zuwa hannu. Haka nan, yayin da ƙarin ya danne jijiyar laka zai haifar da ciwo, zogi, rauni ko rashin ƙwarin wani yatsa / yatsun hannu.
- Yaushe ya kamata a tuntuɓi likita? Za a tuntuɓi likita ne da zarar ƙarin ya fara haifar da alamun da muka ambata a sama domin bin hanyoyin magance ƙarin da suka haɗa da: zuƙe ruwan cikin ƙari da sanya maganin da zai ƙafar da ruwan ƙarin, haka nan, ana yin tiyata domin cire ƙarin daga tushensa, da sauran hanyoyi.
Bugu da ƙari, likitocin fisiyo na taka rawar gani kafin da bayan tiyatar wajen magance matsalolin ciwo, raunin / rashin ƙwarin yatsu ko hannu da kuma magance matsalar tabon tiyata da sauransu.
- Har wa yau, im ma ƙarin ba ya ciwo amma ka damu da munin sifar da ƙarin ya janyo maka, to kana iya zuwa asibiti don a cire shi.