
Daga Ibraheem El-Tafseer
A kwanan nan ƙwacen shafin sa da zumunta na Facebook da WhatsApp, wanda a turance ake kira ‘Hacking’ ya zama ruwan dare, mafi yawan mutane sun rasa ta yaya hakan yake faruwa. To yanzu za mu ɗan yi bayanin yadda mutum zai kare kansa da faɗa wa tarkon waɗannan masu kutsen. Bari mu fara da Whatsapp, wanda mutane daya wa suke mamakin, wasu mutanen kuma suke ganin kamar ba zai yi yu a ƙwace shi ba, saboda lambar waya kaɗai ake amfani da shi wajen buɗewa kuma mafi yawan mutane basu damu da yin hira ‘chatting’ da mutanen da basu san su ba a WhatsApp ɗin. Wasu har sukan iya cewa ma ta ina Bature zai samu lambar su har ya iya ƙwace musu WhatsApp? Shin ta yaya ma zai fara? Da dai wasu tunani da suka dogara da su na ƙin yarda ana iya ƙwacewa.
Duk da cewa yanzu an fara ganin zahiri cewa ana iya ‘Hacking’ ɗin WhatsApp ɗin, kuma wasu ma an musu, to wane mataki ya kamata a ɗauka dan ganin an daƙile faruwar hakan nan gaba?
Hanya mafi sauƙi da za ka bi don daƙile yi maka kutse a WhatsApp ɗinka shi ne, ka shiga ‘SETTING ‘ a cikin WhatsApp ɗin naka, sai ka shiga ‘TWO STEP VERIFICATION’ ka saka shi.
Yaya ake saka two step verification a WhatsApp?
Idan ka shiga ‘settings’ ka duba ‘account settings’ a ciki za ka ga ‘Two Step Verification’ sai ka shiga ka saka abin da suka tambaya, sannan kuma za su buƙaci ka saka Email ɗinka domin toshe duk wani yunƙuri na yi maka kutse a WhatsApp ɗinka.
TA YAYA ZA KA KARE KANKA DAGA MASU ƘWACE SHAFIN FACEBOOK?
Mafi yawan mutane idan sun buɗe shafi a sahar Facebook ba sa la’akari da seta wasu abubuwan, musamman waɗanda suka shafi layin tsaro kamar ɓoye wasu muhimman sirruka game da mutum kansa.
wasu daga cikin mutane idan sun buɗe shafin Facebook, sukan yi amfani da makullan sirri mafi sauƙi ta yadda ba za su taɓa mantawa ba, mafi rinjaye daga cikin su, suna amfani da lambobin wayar su lambar kuma wanda suka riga suka yi rijista wajen buɗe shafin Facebook ɗin dashi.
Shin laifi ne amfani da lambar waya a matsayin makullin sirri ‘password’? A’a ba laifi ba ne amma akwai buƙatar ɓoye lambar wayar daga masu buɗe ko bincika shafin ‘profile’ ɗin mutane don ganin sirrukansu ko samun lambobin su.
Yana da matuƙar muhimmanci mu san cewa masu kutse cikin shafin mutane na Facebook, mafi yawa daga cikin su ta hanya mafi sauƙi suke iya shiga, shi ne rashin tsaro da kuma rashin ba da muhimmancin da muke yi wa shafin na Facebook. Daga mun fara amfani da shafin muna ‘chatting’ shikenan bamu damu da kulawa ba.
Abubuwan da ya kamata mu kiyaye sun haɗa da ɓoye sirrukan mu masu muhimmanci irin su lambar waya, Email, shekarun haihuwa (Date of Birth) da sauransu, kuma muke yawan ƙara saka masa tsaro musamman akwai abubuwan da ake kira code generator, two factors authentication da sauransu.
Ya kamata kuma kasan ‘where you’re logged in’ ko da za ka sayar da wayar ka to ka tabbatar ka sauke shafinka na Facebook daga cikin wayar. Wato za ka yi log out kenan. Sannan yana da kyau idan za ka canza waya ka goge dukkan abin da ke kan wayar ta hanyar shiga setting na kan wayar, sai ka shiga ‘factory data reset’.
Mutane da dama suna yawan kuka da yadda ake ƙwace musu shafinsu na Facebook, alhali shafin yana da muhimmanci a wurin su, wasu na da abokai makusanta da waɗanda ke nesa, kamar ƙasashen waje, kuma ta wannan sahar Facebook ɗin ce kaɗai suke haɗuwa, wasu kuwa sun shahara da shafinsu na Facebook ɗin, ma’ana suna da mabiya da yawa wanda lalacewar shafin kan iya haifar musu da matsala ta rashin dawo da wasu cikin mabiyan nasu, ko wani al’amari na siyasa ko kasuwanci da suke tallata wa ta shafin nasu na Facebook.
Sau da yawan lokuta mutane sukan buɗe shafin Facebook haka kawai ba tare da bin matakai na Facebook ɗin ba, daga sun buɗe shafin Facebook ɗin, sukan fara amfani da shi ne kai tsaye ba tare da tunanin seta wasu abubuwa da zai sauƙaƙa musu amfani da Facebook ɗin ba, ko kuma ƙaƙaba wa shafin tsaro mai yawa domin kiyaye lafiyar shafin Facebook ɗin daga baragurbin mafarauta (Hackers) ba.
Daga lokacin da mutum ya bar shafinsa na Facebook haka kawai ba tare da tsaro ba, ta hanya mai sauƙi za’a iya kutsawa a ɓata masa shafin nasa, ko a maka ƙwacen shafin Facebook gabaɗaya, sai dai ka ga ana saka abubuwa a shafin naka kai kuma baka sani b, ko kuma ka ga an tura roƙon kuɗi a wajen jama’a har da waɗanda kake jin kunya da ganin girmansu.
Lokacin da aka ƙwace wa mutum shafinsa na Facebook, abu na farko da suke yi shi ne canza wa mutum makullin sirri ‘password’ sannan su shiga su canza duk wata hanya ko kafar da za a iya bi don dawo da shafin, bayan nan sai su goge duk wani rubutu ko hoto da ke cikin shafin Facebook ɗin (amma idan sun ga dama, domin ba kowane a cikinsu ke yin hakan ba), canza wa mutum hoton dake akan ‘Profile’ ɗinsa shi ne abu na ƙarshe da suke bayan sun canza wa mutum suna.
Wannan kuwa yakan ba da wahala sosai wajen dawo da shafin Facebook ɗin. Ko da an yi nasarar ƙwato shafin naka, to wasu abubuwan ma basa dawowa, sai dai daga qarshe ka ji mutum yana cewa ba ya jin daɗin shafin nasa na Facebook ɗin.