Ciyo Bashi, ba Alheri bane…. Inji Alhaji Sabo Musa, S.A Restoration…

Zaharaddeen Ishaq Abubakar @Katsina City News

Mai taimakawa Gwamnan Katsina Alhaji Aminu Bello Masari, akan maido da Al’amura akan dai-dai wa daida, Alhaji Sabo Musa, yayi tsokacin ne a wajen Bikin aza harsashin wasu muhimman Ayyuka wanda dan majalisar tarayya mai wakiltar Katsina Hon. Salisu Iro Isansi yayi a ranar Lahadi, S.A na Gwamna yayi Martani ga masu bata sunan Gwamnatin Katsina, da Gwamna Aminu Masari akan wasu da suke haɗa ginin Tarihi na Shatale-talen sabuwar tasha a cikin garin Katsina da wasu gadoji, dake wasu jahohi, inda suke cewa, iya abinda Gwamnatin jihar Katsina tayiwa Al’uma kenan.

Alhaji Sabo Musa yace, duk jihohin da suke wannan abin aje a binciki irin dumbun bashikan dake kansu, amma mu a Katsina bamuci bashin ko sisi ba, kuma duk da haka babu wani Wards ko Mazabu, inda wannan Gwamnatin bata shiga ta gina ko ta gyara, makarantu ba, kuma kowa yasan irin halin da wannan gwamnatin ta iske Ilimi da makarantun, da matsalar tattalin arziki, gami da annobar korona, amma masu ciwo bashin, sun ciwo bashi alokacin da Dala, tana farashi mai sauƙi, amma bashin akansu, Dala ta lillinka Naira, jihohin dake da wannan bashin, bazasu iya biya ba, Inji Alhaji Sabo musa.

An gudanar da tarukan dora muhimman ayyukan ne a Unguwar Malali, inda dan Majalisar ya dora Harsashen ginin, makarantar Firamare, da makarantar makafi, inda anan ma aka dora harsashin ginin, dakunan karatun dalibai. Sai titin da ya taso daga Mobil zuwa Rafin dadi, ya dire a Shatale-talen kofar yandaka, sai kuma, wanda ya tashi daga, kofar Durbi, ya shiga Unguwar Malam Niga zuwa kofar Marusa, dakuma, sabuwar hanyar da Ta tashi daga bakin gidan man Danmarna zuwa unguwar Kanada, ta isa bayan gidan Rodi.

Al’uma sun yaba da wadannan gagaruman ayyuka, inda suka yi son barka,

A wajen jawabin sa Kwamishinan Ilimi da ya wakilci Gwamnan Katsina, Farfesa Badamasi Lawal, yace: wannan aiki ba karamin cigaba bane, kuma taimakawa Gwamnatin jihar Katsina ne, domin raya kasa, Kwamishinan ya kara da cewa, a iya sanin sa ‘yan majalisa biyu ne yaga suna irin wannan aiki a fadin jihar katsina yana fata saura zasuyi koyi da Salisu Iro Isansi.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here