Daga Ukasha Ibrahim
Wani mafarauci mai suna Usman Alhaji Audu ya kashe kansa da kanshi ta hanyar harbin kansa da bindiga da gangan sakamakon mahaifiyar shi tayi mishi fada akan yadaina dukan yaron shi karami ‘dan shekaru 4 a duniya ba gaira ba dalili.
Marigayin wanda ya kasance ‘dan kauyen Gada Maisaje a karamar hukumar Gombi dake jihar Adamawa, mahaifiyar tashi tayi mishi fada akan yadaina dukan yaron nashi wanda hakanne ya fusata marigayin inda ya dauko bindigan shi wanda yake zuwa farauta dashi ya harbe kanshi har lahira…
Kamar yadda kakakin yan sandan jihar Adamawa suleiman Yahaya Nguroje ya shai dawa Yola 24 faruwar lamarin ta wayar tarho, Mahaifiyar marigayin ta ce dan nata mai suna Usman alhaji Audu ya kashe kanshi ne a ranar Laraba wanda yazo dai-dai da 19 Oktoba 2022 bayan yaron marigayin ‘dan shekaru 4 kacal a duniya ya fita yawo bai dawo da wuri ba ,dawowar shi ke da wuya mahaifin nashi wato marigayi Usman alhaji Audu ya fusata inda ya nufi kan yaron ya fara dukanshi baji ba gani.
Hakan yasa mahaifiyar tashi tazo tayi mishi fada akan yadaina dukan yaron kada ya illa ta shi Wanda hakan yayi matiukar ‘bata wa shi marigayin rai yace da ita bazai iya jurar wanan abin takaicin ba saboda haka kawai zai kashe kanshi ya huta
Daga nan ya nufi dakin shi cikin sauri yafito da bindiga ya harbi kanshi a ciki nan take ya fadi , duk da an kaishi asibiti dake cikin garin Gombi domin kokarin ceto rayuwar shi amma hakan bayyiwu ba….