Advert
Home Sashen Hausa CIKEKKEN RAHOTON ZAMAN KOTUN SHEIKH ZAKZAKY DA GWAMNATIN KADUNA. (2) Al'hamis 19/11/2020.

CIKEKKEN RAHOTON ZAMAN KOTUN SHEIKH ZAKZAKY DA GWAMNATIN KADUNA. (2) Al’hamis 19/11/2020.

CIKEKKEN RAHOTON ZAMAN KOTUN SHEIKH ZAKZAKY DA GWAMNATIN KADUNA. (2) Al’hamis 19/11/2020.

Salam ‘yan uwa barkanmu da dawowa babbar kotun jihar Kaduna don ci gaba da shari’ar Shaikh Zakzaky da matarsa Malama Zeenatuddin Ibrahim.

Yanzu haka lauyoyin dukkan bangarorin sun halara a kotu. Alkali ya iso an kira shaida na uku a wannan shari’a. Sunan wannan shaida Muhammadu Abba Girei, wanda tsohon Darakta ne a hukumar tsaro ta farin kaya wato DSS.

Kamar kullum AU Tumburkai ne zai kawo muku abubuwan da za su gudana kai tsaye.

Lauyan gwamnatin Jihar Kaduna, Bayero Dari ya nemi Girei ya fada wa kotu cikakken sunansa da in da ya yi aiki na karshe. Ya ce Sunan sa Muhammadu Abba Girei kuma aikinsa na karshe shi ne Darakta Oparation a hedikwatar DSS da ke Abuja.

Ko ka san Shaikh Zakzaky da matarsa? Ya ce eh ya san su sosai kuma lokacin da aka kawo su hukumar tsaro a shekarar 2016. Ni ne ke kula da al’amuransu, wato ciyar da su da kuma yi musu hidima. Ya ce lokacin da suke hannun mu, wasu masu bincike na ‘yan sanda sun zo daukar bayanansu Amma suka ki yarda da hakan. Wanda kuma ni ban san dalilin da ya sa Shaikh Zakzaky da matarsa Malama Zeenatuddin Ibrahim suka ki yarda ba.

Su wa suka mika muku Shaikh Zakzaky da matarsa Malama Zeenatuddin? Ya ce sojoji ne suka mika su. Kana ina lokacin da ‘yan sanda suka zo neman bayanansu kai kana ina? Ya ce, ina asibiti tare da su Malam Zakzaky da matarsa Malama Zeenatuddin. Bayero Dari ya kammala tambayiyin sa.

Femi Falana SAN ya tambayi Girei cewa lokacin da aka kawo su Malam da Malama a wane hali ka gansu, shin suna cikin koshin lafiya? Girei ya ce; ban sani ba, saboda ni ba likita bane. Wace rana aka kawosu? Ranar 15/12/2015 aka kawosu amma ni a ranar 16/12)2015 ne na fara ganinsu.

Ka tabbata ranar 16/12/2015 ka gansu? Ya ce ko ka ga jini a jikinsu lokacin? Ya ce bai gani ba. Shin ka san lokacin idon Malam a fashe ya ke? Ya ce ba zan iya tunawa ba. Sun ce maka akwai harsasai a jikinsu wanda a lokacin ba a ciresu ba? Ya ce ba zan iya tunawa ba.

Lokacin da ka gansu a Asibiti an kwantar da su ne? Ya amsa da cewa ba a kwantar da su ba. Sai Alkali ya ce ba za ka iya tunawa ankwantar dasu ko ba kwantar da su ba? Ya ce ba zan iya tunawa ba. Shin ko ka san sun kwashe watanni a asibiti a kwance. Ya ce ba zan iya tunawa ba. Ko ka san cewa yan sandan da suka zo ganin su AIG Rasheed ne? Ya ce ba zan iya tunawa ba. A takardar da ka rubuta ta shaida ka ce lokacin da AIG Rasheed ya zo daukar bayanansu lokacin suna farfadowa daga raununkan da suka samu ne shiyasa ba su iya ba shi bayanan ba, shin ka san ka fadi hakan? Ya ce ba zan iya tunawa ba. Wane lokaci ka dauka tare da su? Ya ce daga 2015 zuwa 2016 in da aka yi masa transfer zuwa Bayelsa. Amma ba zai iya ko wace rana bane. Ko ka san cewa a October aka yi maka transfer zuwa Bayelsa? Ya ce ban sani ba. Ranar 2 ga Disamba kotun tarayya da ke Abuja ta yanke hukuncin cewa a sake su. Ko ka san da wannan hukuncin? Ya ce ban sani ba.

Ka ce an kawosu ranar 15/12/2015 ko a akwai wata oda da kuka samu na tsaresu? Ya ce ban sani ba. Ko ka san gwamnatin Jihar Kaduna ta kafa kwamitin bincike kan abin da ya faru a Zaria? Ya ce ban sani ba. Ko ka san DSS sun hana wadanda ake kara bayyana a gaban JCI? Ya ce ban sani ba.

Ka bayyana cewa jami’an tsaro na yan sanda sun zo daukar bayanan Malam da Malama in da Malam ya shaida musu cewa ba zai ce komai ba har sai an zo da Lauyoyinsa? Ya ce ban sani ba.

Yanzu kana cewa duk wanda DSS suka kama asibiti ake ajeye shi ko da lafiyar sa lau? Ya amsa da cewa eh haka suke yi. Al’adarsu ne hakan. Shin ka san cewa ni Lauyan Malam sun Sha tsareni a DSS? Ya ce bai sani ba.

Shin ba ka taba karantawa ba cewa an tsareni a DSS? Ya ce eh ban taba ba. Alkali ya sa baki, ya ce ko a jarida ba ka taba karantawa ba? Ya ce bai taba ba kuma bai taba ji ba. Falana ya ce a shekarar 1992 an kama ni ni da Cif Gani Fahewunmi in da ake tuhumar mu da cin amanar kasa kuma kana cikin masu bincike? Ya ce bai sani ba.

Falana SAN ya kammala tambayarsa. Lauyan Malama ya ce ba shi da wata tambaya. Kotu ta sallami Girei.

Shaida na hudu a wannan shari’a ya shigo mai suna Muktar Gambo.

Sunana Muktar Gambo ina zaune ne a Madaki road Gyallesu, sana’ata daukar hoto kuma nine mataimakin shugaban kungiyar matasan Gyallesu. Kuma sakatare a Gyallesu Vigilant Community

Ko ka san Shaikh Zakzaky da matarsa Malama Zeenatuddin? Ya ce ya san su saboda a Unguwa daya suke zama. Kana da wata danganta da su bayan ta zama Unguwa daya? Ya kasa amsa tambayar. Lauya Bayero ya canza tambayarsa zuwa cewa shin wane irin zama kuke yi da shi? Ya ce shekaru biyu da dawowar Shaikh Zakzaky Unguwar muka Fara samun matsala da shi. Kuma ya dawo Unguwar ne a shekarar 1998.

Ko za ka fadawa kotu irin matsalar da kuke samu da shi? Ya ce matsalar ita ce bayaba yan banga hadin kai kuma ba sa barin masu kayan Sarki irin yan sanda da soji shiga Unguwar. Don haka Unguwar ta zama dabdalar masu aikata miyagun laifuka.

Ko za a iya fada wa kotu cikakken sunan mabiya Shaikh Zakzaky? Ya ce sunansu Shi’a. Ko zaka iya lisafta yawansu? Ya ce ba zan iya ba saboda suna da yawa. Ko kun taba kai koke wurin hukuma? Ya ce mun kai koke wajen Hakimi kuma suka tafi wurin Malam Zakzaky tare da Hakimi da suka je Malam ya shaida musu cewa bai sani ba. Amma zai dauki mataki. Amma ba a yi komai ba.

Me za ka ce wa kotun kan Malam da Malama? Ba ma son zamansu a Gyallesu. Saboda suna hana mutane shiga Gyallesu sun hana wani Navy Commander shiga gidan mahaifinsa sun hana gwamnan Kaduna Ramalan Yero shiga Gyallesu. Bayero ya kammala tambayiyin sa.

Falana SAN ya tambayeshi ko kai musulmi ne? Ya ce eh. Ko kai dan Shi’a ne? Ya ce shi ba shi’a ba ne. Ko kai Sunnah ne? Ya ce eh. Ko ya san Sunnah suna yaƙar Shi’a? Ya ce bai sani ba. Shin ka ce ba ka son zamansu a Unguwar? Ya amsa da cewa eh ba ya so. Ko ka san a an rusa gidan Shaikh Zakzaky a Gyallesu? Ya ce eh na sani. Ko ka san an yi rikicin siyasa a 2011 lokacin da Buhari ya fadi zabe? Ya ce eh na sani.

Lokacin da aka yi wannan rikici Shaikh Zakzaky ya ba kiristocin da ake son kashewa kariya a gidan sa? Ya ce ban sani ba. Ko ka san cewa Shaikh Zakzaky na raba abinci ga al’ummar Gyallesu? Ya ce ban sani ba. Ka ce kai da Hakimi kun ziyarci gidan Shaikh Zakzaky, ka san cewa Buhari ya ziyarci gidan Shaikh Zakzaky don yin kamfe? Ya ce ban sani ba. Ko ka san Malam Nasiru Elrufai ya ziyarci gidan Shaikh Zakzaky don yin kamfe? Ya ce ban sani ba. Kana cikin yan bangar Gyallesu, shin kuna kula da Unguwar awa 24? Ya ce eh. Shin kasan a shekarar 2014 an kashe ‘ya’yan Malam 3? Ya ce eh ya sani. Shin kana da labarin Elrufai ya ziyarci gidan don yin ta’aziyya? Ya ce eh Yana da labarin. Ko ka san Dambazau minista ya je gidan? Ya ce bai sani ba. Ko kana da labarin hukumar kare hakkin dan adam ta ƙasa ta aika wakilai don jajantawa ga Malam a 2014? Ya ce ban sani ba

Shin kasan ‘ya’yan sa da aka kashe? Ya amsa da cewa ya san su a fuska? Kana da labarin ko an hukunta wadanda suka yi kisan? Ya ce bani da labari? Ko ƙungiyar ku ta nema musu haƙƙinsu? Mun dai je mun yi ta’aziyya.

Shin ko kana da labarin a shekarar 2015 an sake kashe ‘ya’yansa uku? Ya ce bani da labari. Ko ka san abin da ya faru da Shaikh Zakzaky a ranar 14/12/2015? Ya ce sojoji sun je gidan Shaikh Zakzaky. Ko ka san sojoji sun kone gidan? Ya ce ban sani ba saboda ina gida kulle.

Zaka iya tuna cewa ka bayar da shaida a gaban JCI? Ya ce eh. Ko ka san cewa JCI ta bayyana cewa mutane 347 aka kashe a Zaria? Ya ce na ji labarin amma ban san ko JCI ce ta fada ba. Shin ko ka san wani da aka kama ake tuhumar da wannan kisan? Ya ce ban sani ba. Shin kana farin ciki da yanzu ba ‘yan Shi’a a Gyallesu. Ya ce eh ina farin ciki saboda sun sami zaman lafiya.

Falana SAN ya kammala tambayarsa. Lauyan Malama ya ce ba shi da tambaya.

Shamsudeen Aliyu Ahmad ne wani mazaunin Gyallesu zai ba da shaida ta 5. Ya ce shi tela ne da ke dinki a Madaki road Gyallesu. Bayero ko ka san Shaikh Zakzaky da matarsa Malama Zeenatuddin? Ya ce eh na san su saboda shagona yana layi daya ne da gidansu.

Me za ka iya tuna ya faru da kai a wata rana ta asabar a shekarar 2013m Ya ce a shekarar 2013 wata rana ina zaune a shago sai ga yaran Malam da baro sun zo suna kwashe duwatsun da muka tare hanya saboda ƙura na bata mana kayan da muke dinki. Shi ne na ce ba za mu bari su kwashe ba. Suka ce mun sanya dutsinan ne saboda malaminsu. Ina cikin magana da su sai ga mota cike da makamai zan gudu kenan sai suka sare ni a kai. Daga nan sai muka tafi wurin ‘yan sanda muka kai koke. Sai aka kaini asibiti.

Falana SAN ya tambaye shi ko ka san wadanda suka sare ka? Ya amsa da cewa ban san su ba. Falana SAN ya kammala tambayarsa.

Lauyan Malama ya ce bai da tambaya.

Musa Isiyaku shine mai ba da shaida na 6. Ya ce shima mazaunin Gyallesu ne ya ce yana zaune a gida mai lamba 21 Sarkin Yaki Gyallesu.

Ko ka san Malam Isiyaku? Ya ce eh Babana ne.

Ya ce wata rana yaran Malam sun sanya shinge a hanya ba sa barin kowa ya wuce sai wanda suka amince da in da zai je. Wata rana aka dauko wani yaro za a wuce da shi sai yaran Malam suka tare mai babur din amma ya ki tsayawa sai suka jefa musu sanda sai suka fadi, yaron ya karye. Daga nan sai mutanen Unguwa suka ce ba su yarda ba sai an cire wannan shingen. Sai rigima ta barke a wannan Unguwar. Kuma Baba shi ne madakin Unguwar sai aka kira shi ya zo wurin. Babana ya je wurin yana ba mutane hakuri sai wani daga cikin almajiran Malam ya ciro wuƙa ya caka masa a ƙafa. Da suka caka masa wuka sai ya fadi. Sai mutane suka korasu. Sai almajiran Malam suka fara harbin mutane da gwafa. Sai mutane suka gudu. Ni da ƙanina muka ɗauko shi. Muka kai shi asibiti aka yi masa magani muka dawo da shi gida.

Ya ce haka muka yi ta jinya har wata hudu kuma an fada mana cewa wuƙar tana da guba. Don haka daga baya ya ya mutu. Bayero Dari ya kammala tambayarsa.

Falana SAN ya tambayeshi ko kai musulmi ne? Ya ce eh. Sunnah ne shi ko Shi’a? Ya ce shi Sunni ne. Ko ka fada wa yan sanda cewa ga wandanda suka kashe babanka? Ya ce ban kai rahoto ba. Zaka iya fadin wata da ranar da mahaifinka ya rasu? Ya ce ba zan iya fada ba. Ko ka san wanda ya ya caka wa Babanka wuka? Ya ce eh Ina ganinsa a cikin tawagar Malam. Ka san sunan sa? Ya ce sunansa Ruhana. Ko ka san in da ya ke yanzu? Ya ce yanzu bana ganinsa.

Ko kana da labarin cewa a ranakun 12,13,14 ga watan Disamba sojoji sun kai hari Gyallesu? Ya ce eh na sani. Ko ka ga yan Shia a wannan rana eh sun shigo har gidan mu,Sun shigo ne don boyewa? A’a sun zo ƙona mana gida ne. Ko sun kona muku gidan? Ba su ƙona ba. Kana da labarin sojoji sun kone gidan Shaikh Zakzaky kuma suka rushe gidan? Eh ina da labari.

Falana SAN ya kammala tambayarsa.

Lauyan Malama ya ce bai da tambaya.

Bayero Dari ya ce a nan za su tsaya. Suna neman a basu wata rana saboda suna son kawu GOC ne daga Maiduguri.

Falana SAN ya roki kotu da ta ba da ranaku biyu a jere don su kammala kawo shaidunsu a wannan rana.

A ƙarshe dai Kotu ta sanya ranar 25,26 ga watan Janairu don kawo sauran shaidun da suka rage.

KATSINA CITY NEWShttps://www.katsinacitynews.com
Danjuma Katsina, Dan Jarida, Manazarci, Marubuci, Mamallakin Jaridun KATSINA CITY NEWS, JARIDAR TASKAR LABARAI, THE LINKS NEWS, a karkashin Kamfanin MATASA MEDIA LINKS NIGERIAN LTD

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

THE NNEWE – UDUWA ROAD LINKING ENUGU AND EBONYI STATES HAS BEEN COMPLETED! #PositiveFactsNG

https://www.facebook.com/101788642037662/posts/263438592539332/

POLICE PRESS RELEASE NO.01/2022: KATSINA POLICE COMMAND RESCUED SEVEN (7) VICTIMS OF HUMAN TRAFFICKING

CZ: 5250/KTS/PPRO/VOL.5/XX ………………………………………………………… ………………………………………………………… POLICE PRESS RELEASE NO.01/2022 KATSINA POLICE COMMAND RESCUED SEVEN (7) VICTIMS OF HUMAN TRAFFICKING: On 20/01/2022 at about 1120hrs, based on credible intelligence, the...

Katsina To Flag Off Basic Healthcare Provision Fund

Katsina To Flag Off Basic Healthcare Provision Fund By Segun Olaniyan ' KATSINA – The Katsina State Contributory Healthcare Management Agency has concluded plans to flag off the...

Plenary proceedings of the House of Representatives for Thursday, January 27th, 2022

The Speaker of the House, Rep. Femi Gbajabiamila presiding. After leading the opening prayer and National Pledge, the Speaker approved the votes and proceedings for...