Cika shekara 22 da rasuwar Mamman Shata
June 18, 2021

DAGA MUHAMMAD LAWAN RANO

A YAU, 18 ga Yuni, 2021 Alhaji Dakta Mamman Shata Katsina, MON, ya cika shekaru 22 da komawa ga Mahaliccin sa. A halin da ake ciki yanzu Shata ya zame wa makaɗa da mawaƙan Hausa dutse ba ka ɗaukuwa sai da gammo, mutsu-mutsu gobe jar kasa, ruwan dare mai gama duniya, ya buga da mazajen farko ga shi ya na bugawa da mazajen yanzu. Abin da maroƙan sa ke faɗa kenan idan zai fara waƙar sa ta Bakandamiya.

Babu wata ƙasa a duniya da za ta bugi ƙirji ita kaɗai ta ce ta samu cigaba a rana guda. Su kan su ƙasashen da su ka ci gaba irin su Amurka, Rasha, Chaina, Birtaniya, Japan da Jamus sun yi amfani ne da kyawawan al’adun su wajen gina tushen cigaban da su ka samu.

Mawaƙa da makaɗan waɗannan ƙasashe da su ka ci gaba sun bada gudunmawa mai yawan gaske ta fuskar irin tasu fasahar wajen ciyar da ƙasashen nasu gaba.

Farfesa Ɗandatti Abdulƙadir, kafin ya zama Mataimakin Shugaban Jami’ar Bayero, Kano, ya rubuta kundin digirin sa na uku ne kan rayuwa da waƙoƙin Alhaji Mamman Shata, wanda ya gabatar ga shaihunan malaman Jami’ar Indiana ta ƙasar Amurka. Wannan yunƙuri na Frfesa Ɗandatti ya ƙara tabbatar da cewa shaharar da Shata ya yi, ba a iya Nijeriya kawai ta tsaya ba har ma da waɗansu ƙasashen.

Cikakken sunan Shata shi ne Muhammadu Lawal. Sunan Mamman laƙabi ne irin wanda kakanni kan raɗa wa jikokin su tun su na yara. Ita kuwa kalmar “Shata”, laƙani ne wanda ake kiran sa da shi lokacin da ya ke cinikin goro. Magaji Salamu Musawa, wanda a lokacin kamar uba ne ga Shata, shi ya raɗa masa sunan “Mai Shata”. Manufar sa ita ce mutum wanda in ya samu abu sai ya ɓatar abin sa, ba ya tattali.

Kafin zuwan Turawa ƙasar Hausa, al’ummar Hausawa na da addinin su na Musulunci, akwai kuma kaɗan da ke bin addinin gargajiya da ake kiran su Maguzawa. Ba a san hikimar rubuta sunayen yara da shekarun su a ajiye don tarihi ba kamar yadda yanzu ake yi. Wannan shi ya sa ba a san cikakkiyar shekarar da za a ce an haifi Alhaji Mamman Shata ba. Amma a shekarar da ya kai ziyara gidan rediyon Muryar Amurka (VOA) a cikin 1989, ya ce shekarun sa 65 a lokacin. Manazarcin tarihin rayuwar Shata, Ibrahim Sheme, ya ƙiyasta a cikin littafin ‘Shata Ikon Allah!’ cewar an haife shi ne a wajen 1923.

Karanta kuma Farfesa Yakasai: Abin da ya sa mu ka yi diwanin waƙoƙin Aminu Ala

Kwalin faifan garmaho na waƙoƙin Shata
Shata ya yi waƙoƙi bila adadin waɗanda har zuwa yanzu tarihi bai kai ga gano yawan su ba. Haka waƙoƙin sa da su ka yi shuhura su ma ba su ƙirguwa, amma ga guda 20 waɗanda mujallar Fim ta zaƙulo domin kafa misali, su ne:

1. ‘Na Gode Wa Bashar Ɗan Musa Mamman Mai Mulkin Daurawa’

2. ‘Na Tsaya Ga Annabi Muhammadu’

3. ‘Ƙusoshin Birni Uwawu’

4. ‘Umaru Ɗan Ɗanduna Na Gwandu’

5. ‘Sarkin Bori Sule’

6. ‘Wamban Kano Habu Ɗan Maje’

7. ‘Bawan Allah Mamman Ɗa’

8. ‘Gagarabadan Namiji Tsayayyen Ɗan Kasuwa’

9. ‘Alhaji Garba ‘Yammama’

10. ‘Sardauna Kakan Ka Ɗanfodiyo, Jikan Gidan Bello Ne Ahmadu’

11. Na Gode Wa Hassan Hadi’

12. ‘Jirgin Sama Bawa Tashi Ƙoli Ka Tsere Na Laraba’

13. ‘Yarinya Lami Shagamu’

14. Na Gode Goshi Ta Ɗangude’

15. Bakandamiya

16. ‘Haji Gaban Bichi Ɗan Shehu’

17. ‘Na Gode Wa Amadun Gaya’

19. Waƙar Indon Musawa

Karanta kuma Dabo Daprof: Abin da ba zan manta da shi ba…
20. ‘Ta Kunya Delun Kunya’

To sai dai al’umma da manazarta a manyan jami’oi’n ƙasar nan, musamman ɓangaren nazarin harshen Hausa, na cigaba da nazarce-nazarce bisa irin gudunmawar da Shata ya bai wa harshen Hausa ta hanyar waƙoƙin sa. Da alama ba za a daina yin nazarin waƙoƙin Shata da rayuwar sa ba har ƙasa ta naɗe.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here