Advert
Home Sashen Hausa Christmas 2020: Tsaron rayuka zai ci gaba da zama shika-shikan imanina -...

Christmas 2020: Tsaron rayuka zai ci gaba da zama shika-shikan imanina – Buhari

Christmas 2020: Tsaron rayuka zai ci gaba da zama shika-shikan imanina – Buhari

Muhammadu Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce matsalolin tsaron da ƙasar ke fama da su, sun fi ƙarfin ‘yan shawarwarin da ake bazawa a gari a matsayin hanyoyin shawo kansu.

A cikin saƙonsa na taya al’ummar Kirista bikin ranar Kirsimeti yau, Shugaba Buhari ya ce zai ci gaba da bin hanyoyi iri daban-daban wajen rage kaifin matsalolin tsaro.

‘Yan Njaeriya da dama ciki har da majalisun tarayyar ƙasar sun yi ta kiraye-kirayen a aiwatar da sauye-sauye cikin harkokin tsaron Nijeriya ciki har da sallamar manyan hafsoshin tsaro.

Shugaba Buhari dai ya ce jazaman ne al’ummar ƙasar su samu ‘yancin yin rayuwa da kuma zirga-zirga ba tare da wani tarnaƙi ba.

Hakan a cewarsa na da matuƙar muhimmanci, ba kawai wajen tabbatar da kwanciyar hankali da hadin kai ba, har ma ga bunƙasar tattalin arziƙi.

Wannan layi ne

Aƙidun Yesu Almasihu

A cikin saƙon nasa, Buhari ya ce bikin Kirsimeti, lokaci ne na murna da zaman lafiya da kyakkyawan fata da nuna ƙauna da taimakekeniya da kuma ceto.

Kuma waɗannan aƙidu da zuwan Yesu Almasihu ya kawo, su ne ake matuƙar buƙata cikin wannan lokaci da ƙasar ke fama da ƙalubalai iri daban-daban ciki har da ƙaruwar hare-haren ‘yan fashin daji da satar mutane don neman fansa da ‘yan ta-da-ƙayar-baya da karayar tattalin arziƙi da kuma ɓarkewar annobar korona.

Buhari ya ƙara yin kira ga ‘yan Najeriya su ƙara amanna da jajircewar gwamnatinsa da kuma duƙufarta wajen dawo da zaman lafiya da tsaro da kuma ƙaruwar arziƙi ga Najeriya.

Shugaba Buhari ya kuma nanata alƙawarin cewa a ƙarƙashin kulawarsa, gwamnatin Najeriya za ta ci gaba da samar da tallafi da arziƙin da Allah ya hore ga dakarun sojin da sauran hukumomin tsaro a ƙoƙarinsu na tunkarar duk wata barazana.

Ya kuma buƙaci su ƙara himma wajen murƙushe ƙaruwar barazanar tsaro musamman a yankuna arewacin da ma a ɗaukacin ƙasar gaba daya.

Ya ce samar da tsaro ga illahirin ƴan Najeriya zai ci gaba da zama wani shika-shikan imani a gare shi.

A cewarsa, zuciyarsa ba za ta iya nutsuwa ba, idan ya yi watsi da wannan muhimmin nauyi na tsare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Shugaban ya ce yakan ji zafi a duk lokacin da aka keta haddin zaman lafiya da tsaro a kowanne sashe na ƙasar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

PHOTOS: Buhari Receives Turkish President Erdogan, Wife in Abuja

The President, Major General Muhammadu Buhari (retd.), has received the Turkish President, Recep Tayyip Erdogan and his wife, Emine at the State House in...

Gwamnatin Kaduna ta ce an kashe mutum 343 cikin wata uku a jihar

Daga: Comrade Musa Garba Augie. Gwamnatin Jihar Kaduna ta tabbatar da mutuwar mutum 343 sakamakon ayyukan 'yan fashin daji da sauran tashe-tashen hankali cikin wata...

Shekarau ba uban Gidana bane A siyasa ,,,, Abokin Siyasa Tane Kawai ,, Cewar Musa Iliyasu Kwankwaso…

Ni Bana Adawar Cikin Gida Amma Duk layin Dayake Na Gaskiya Shinake bi Kuma Layina Shine Abdullahi Abbas,,, Cewar Musa iliyasu Kwankwaso, Saidai Yayi tsokaci...

RIKICI TSAKANIN MAHDI SHEHU DA GIDAN REDIYON VISION FM KADUNA!

  Musa Ibrahim daga Kaduna @Katsina City News Wani rikici ya barke tsakanin malam mahadi shehu shugaban rukunin kamfanonin dialogue da kuma gidan rediyon vision FM...

BREAKING: Police arrests EndSARS protesters in Lagos

The Police in Lagos State are arresting EndSARS protesters at the Lekki toll gate. One of them has been identified as Okechukwu Peter. His phone...
%d bloggers like this: