Advert
Home History CHE GUEVARA: ALAMIN GWAGWAMARYA A QARNI NA 20

CHE GUEVARA: ALAMIN GWAGWAMARYA A QARNI NA 20

MBI

Wane Ne Che Guevara?

A gurguje za a iya cewa, an samu baki biyu kan takamammiyar ranar haihuwarsa. Takardar haihuwarsa ta ba da shaidar cewa an haife shi ne a ranar 14 ga Yuni, 1928. Amma mahaifiyarsa ta ce wa wani masanin taurari, ta haife shi ne a ranar 14 ga Mayu, 1928. Shi ne na farko cikin ‘ya’ya biyar da mahaifinsa Ernesto Guevara Lynch ya haifa tare da mahaifiyarsa Celia de la Serna Llosa. An haife shi a lardin
Rosario Santa Fe da ke qasar Argentina, qabilar Spaniya wadanda ke da tushe daga Irish.

Mahaifansa matsakaita ne a wadata. Amma an ce tun yana yaro Che Guevara ya taso da qaunar talakawa da tsanar masu kudi. An ce mahaifinsa yakan ce, “wannan zafin nama da rashin gajiya na dansa Che Ghevara, ya samo asali ne daga jinin Irish masu aqidar ‘na qi’.

Tun yana matashi mai karatun likitanci ya yi yawo a tsakanin qasashen kudancin Amurka a keke. Zuciyarsa ta cika da tsanar ‘yan jari hujja sakamakon abubuwan da ya gani na yunwa da talauci a tsakanin akasarin jama’a a wannan tafiya da ya yi. Ya kuma qudiri aniyar taimakonsu. Tun daga nan ya fara gwagwarmayar qwato ‘yancin marasa qarfi. Wanda hakan ne ya hada shi da Raul da Fidel Castro, har suka qaddamar da juyin juya halin da ya tuntsirar da gwamnatin Fulgencio Batista na Cuba wacce Amurka ke mara wa baya. Ya kuma taimaka wurin kyautata alaqar Cuba da Rasha, kasancewarsa mabiyin aqidar Gurguzu.

Duk da cewa shi da kansa ya ce haduwarsa da Fidel Castro ta ba shi natsuwa domin ya samu irin jagoran da yake nema, duk da hakan, bai ci gaba da zama a Cuba bayan nasarar juyin juya halin fiye da shekaru kadan ba. Ya riqe manyan muqamai a Cuba bayan an kafa gwamnati, kusan har ta kai ana masa kallon tamkar shi ne mataimaki. Amma a shekarar 1965 ya bar dukkan daular da yake ciki ya sake komawa fagen gwagwarmaya.

Ya tsallako nan Afirka, qasar Congo don yaqar zaluncin Mobutu Seseko, sai dai shi da abokan gwaminsa ba su samu nasara ba. Ya koma qasar Bolivia da nufin ci gaba gwagwarmaya. A can ne ya gamu da aljalisa a hannun dakarun da CIA ke marawa baya na shugaban qasar ta Bolivia.

Ta fuskar ilimi da fikira, ba kamar Frantz Fanon ba, an fi sanin Che Guevara da karance-karance zalla. Shi haziqin mara nawar makarancin litattafai ne. An samu sama da litattafai dubu uku a kan fannoni daban-daban a gidansa. Yakan yi yawo da takarda da abin rubutu, duk abin da ya karanta sai ya rubuta fahimtarsa a kai. Ya yi nitso a karatun litattafan baitocin waqe, da falsafa, da Buddhanci. Kazalika ya yi bita da nazarin litattafan irin su Bertrad Russell, Sigmund Freud, Jack London da Friedrich Nietzsche. Kuma ya fi son darussan Falsafa, Lissafi, Injiniyanci, Siyasa, Nazarin Halayen mutane da Ilimin ma’adinan qasa.

Iyakar karatunsa dalibta a fannin likitanci wanda ya yi watsi da shi tun kafin ya kammala saboda abin da idonsa ya gani na talauci da yunwar da jama’ar qasashen kudancin Amurka suke fama da su a lokacin da ya yi jaula a tsakanin qasashen. Da kansa ya ce: “Abubuwan tausayin da na gani na wahalar da jama’a ke fama da ita suka sa na bar bangaren likitanci na kama na gwagwarmayar siyasa.”

A ranar 9 ga Oktoba ne Che Guevara ya cika shekara 52 da rasuwa. Duniya ba za ta manta da hoton nan nasa da ke qasa ba, wanda ya zama alami na gwagwarmayar masu neman ‘yanci da yaqar zalunci.

Ernesto Che Guevara ya zamo alamin gwagwarmaya a qarni na 20. “Ba zan huta ba har sai na ga an tarwatsa wadannan turaku na jari-hujja,” maganarsa ke nan cikin wata wasiqa da ya aike wa gwaggonsa, Beatriz, a ranar 10 ga Disamba, 1953.

Saboda murnar sararawa daga fitinar naci a kan yaqin qwatar ‘yanci ta Che Ghevara, an ruwaito Daraktan CIA Richard Helms na lokacin, yana bayyana wa Sakataren gwamnatin Amurka cikin sururi cewa, “An kashe Guevara!”

Fidel Castro na Cuba, ya ayyana zaman makoki na kwanaki uku a qasarsa don nuna alhini a kan rashin kwamred dinsa. Ya ce wa mutanen qasar: “Idan muna son fada wa yaranmu na gobe abin da muke son su zama, dole ne mu ce mu su, ‘ku zama tamkar Che Guevara.'”

A bayan an ci galaba a kansa, an ruwaito cewa, sai Che Guevara ya kalli idon wanda ya zo kashe shi amma bai nuna alamar hakan ba, “Na san cewa ka zo kashe ni ne. Ka kashe kawai ya kai matsoraci! Ba wani za ka kashe ba face namiji!”

A wata doguwar maqalarsa mai taken: Who Was Che Guevara? Marubuci Mark Oliver, ya ce: “Sun kashe mutumin, amma ba su kashe fikirarsa ba. Zuwa wannan lokaci (shekara 52 da rasuwarsa), Ernesto Che Guevara ya ci gaba da rayuwa a matsayin alamin nuna qiyya ga tsarin jari-hujja a kowane lungu na duniya.

©Jarida Radio
16/10/2021

KATSINA CITY NEWShttps://www.katsinacitynews.com
Danjuma Katsina, Dan Jarida, Manazarci, Marubuci, Mamallakin Jaridun KATSINA CITY NEWS, JARIDAR TASKAR LABARAI, THE LINKS NEWS, a karkashin Kamfanin MATASA MEDIA LINKS NIGERIAN LTD

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

THE BUHARI ADMINISTRATION SUPPORTS THE LAGOS STATE RAILWAY PROJECT!

https://www.facebook.com/101788642037662/posts/232549375628254/

Kotu ta rushe shugabacin jam’iyar APC ɓangaren Ministan Ilimi, Adamu Adamu a Bauchi

Babbar kotu a Jihar Bauchi ta rushe shugabacin Babayo Ali Misau na jam'iyar APC a jihar. Rahotanni sun baiyana cewa shi dai Misau yaron Ministan...

2023: Don’t Allow Politicians to Use You, Atiku Group Tells Youths

2023: Don’t Allow Politicians to Use You, Atiku Group Tells Youths editorDecember 5, 2021 4:50 Pm Francis Sardauna in Katsina Ahead of the 2023 general election, the...

‘Yan Bindiga Sun Tsananta Kai Hare-hare Akan Hanyar Gusau Zuwa Shinkafi

Daga Dauda Umar Januhu 'Yan Bindiga a jihar Zamfara suna cigaba da kai zafafan hare-hare tare da sace mutane akan babbar hanyar da ta tashi...

DSS sun kama Janar Dambazau a Kano…

DSS sun kama Janar Dambazau a Kano Jami'an Ƴan sandan Farin Kaya, DSS sun kama Janar Idris Dambazau, Shugaban Hukumar Kare Haƙƙin mai Sayan Kaya...