Advert
Home Sashen Hausa CHANJIN SHEKA DAGA JAM'IYYAR PRP ZUWA BABBAR JAM'IYYAR ADAWA TA PDP, A...

CHANJIN SHEKA DAGA JAM’IYYAR PRP ZUWA BABBAR JAM’IYYAR ADAWA TA PDP, A MALUMFASHI KATSINA

CHANJIN SHEKA DAGA JAM’IYYAR PRP ZUWA BABBAR JAM’IYYAR ADAWA TA PDP, A MALUMFASHI KATSINA

Da safiyar yau ne Talata jam’iyyar PDP ta karamar hukumar Malumfashi ta yi gangamin amsar Hon. Jafar Aliyu, Babban jigo a jam’iyyar PRP ta jihar Katsina hade da dubbin magoya bayan shi su 2240, Shine ďan takarar kujerar majalisar wakilai ta tarayya mai wakiltar kananan hukomomin Malumfashi da Kafur a karkashin tutar jam’iyyar PRP a 2019. Taron wanda aka gudanar a ofishin jam’iyyar PDP na karamar hukumar Malumfashi, Taron ya sami halartar ďimbin al’umma daga jihar Katsina da wajan katsina

A lokacin da yake jawabi, shuganan jam’iyyar PDP na karamar hukumar Malumfashi Hon. Muhammad Abubakar Mainasara Yammama, ya bayyana shigowar Hon. Jafar Aliyu cikin jam’iyyar PDP a matsayin wata babban nasara ga jam’iyyar, kasancewar sa jajirtacce mutum kuma mai kishin ci gaban al’umma. Kuma ya tabbatar da cewa jam’iyyar ta amshi Hon. Jafar Aliyu da hannu bibiyu ba tare da nuna masa wata wariya ba.

Hon. Jafar Aliyu ya bayyana cewa abin da ya ja hankalinsa har ya yanke shawarar shigowa jam’iyyar PDP shi ne, ganin ýaýan jam’iyyar PDP suna da aķidar taimakon talaka kamar yadda Malam Aminu Kano da Alhaji Balarabe Musa suke, waďanda kuma aķidar tasu ce ta sa tun farko ya ďauki jam’iyyar tasu ta PRP ba tare da ya nemi shawara daga kowa ba. Kuma ya yi alkawarin ba da dukkan gudunmuwa don samun nasara PDP.

Hon. Salisu Lawal Uli mataimakin Shugaban jam’iyyar PDP na jihar Katsina, Wanda shine ya wakilci Shugaban jam’iyyar PDP na jihar Katsina , kuma shi ne ya miķa katin jam’iyyar PDP ga Hon. Jafar Aliyu, ya tabbatar da cewa za su bai wa Hon. Jafar Aliyu duk wata dama da ake ba ýaýan jam’iyyar PDP, kuma za su yi tafiya tare da shi kafaďa da kafaďa don ķara bunķasa jam’iyyar PDP a karamar hukumar Malumfashi da jihar Katsina baki ďaya.

Manyan baķin da suka halarci taron sun haďa da Sakataren jam’iyyar PDP na jihar Katsina Hon.Sanusi wali funtua, Shugaban jam’iyyar PDP na yankin Funtua Alhaji Adamu Iliyasu, Alhaji Hadi Mai dawa Elder, Alhaji Yakubu Wada, Alhaji Muntari Kent show, Alhaji Umar Makaurachi, Hon. Umar Haruna Doguwa tsohon kwamishinan ilimi na jihar Kano, kuma tsohon Shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano, Hajiya Bilkisu BCJ, Madam Maman Kuka, Hon. Musa Adamu, Alhaji Sani Shehu Idris Gusau da makamantansu. An yi taro lafiya kuma an tashi lafiya.
*Comr.Mai-Iyali PDP Media*
10.11-2020

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

VICTIMS OF KIDNAPPINGS IN BATSARI REGAIN FREEDOM AFTER 66 DAYS IN CAPTIVITY.

From Misbahu Batsari. Some of the victims of kidnappings were this Friday 23-07-2021 release from captivity in Batsari after spending 66 days in the hands...

Just In: Plane Crash Lands In Kwara, Passengers Evacuated

Many passengers, including some highly placed Nigerians, narrowly escaped death after an aircraft belonging to one of the major airlines crashed upon landing in...

Yar’Adua: I’ll Resist Attempt to Impose Guber Candidate on Katsina Citizens

Francis Sardauna in Katsina A chieftain of the ruling All Progressives Congress (APC) in Katsina State, Senator Abubakar Sadiq Yar’Adua, yesterday vowed to resist any...

Mansurah Isah Ta Yi Allah-ya-isa Kan Mutuwar Auren Ta

DAGA IRO MAMMAN “Allah ka saka min. Allah abin da su ke min ka yi musu, ka yi wa yaran su, iyayen su, ‘yan’uwan su....
%d bloggers like this: