Home Sashen Hausa CETO ƳAN MATA 26 DAGA GWAMNATIN ZAMFARA TAYI SAI DA MUKA BIYA...

CETO ƳAN MATA 26 DAGA GWAMNATIN ZAMFARA TAYI SAI DA MUKA BIYA MILIYAN SHIDA DA DUBU ƊARI SHIDA-mutanen ƙauyen Ɗan’aji

CETO ƳAN MATA 26 DAGA GWAMNATIN ZAMFARA TAYI SAI DA MUKA BIYA MILIYAN SHIDA DA DUBU ƊARI SHIDA-mutanen ƙauyen Ɗan’aji

Kasa da sa’o’i ashirin da hudu da Gwamnatin Jihar Zamfara ta bada sanarwar ceto wasu mata ashirin da shidda (26) wadanda ‘yan ta’adda suka dauke daga kauyen Dan-Aji dake karamar hukumar Faskari ta hanyar tattaunawa da ‘yan ta’addan ba tare da biyan ko sisi ba, sai ga shi al’ummar garin sun musanta wannan labarin tare da bayyana cewa sai da suka hada zunzurutun kudi har Naira Miliyan Shidda da Dubu Dari Shidda (N6,600,000) suka ba ‘yan ta’addar kafin a sako matan.

A jiya dai ne Kwamishinan Ma’aikatar kula da Harkokin tsaro da lamuran cikin gida na jihar Zamfara Alhaji Abubakar Mohammed Dauran ya kawo wadannan mata gaban Maigirma Gwamna Aminu Bello Masari kamar yadda muka sanar a baya, tare da bada bayanin cewa an amso sune ta hanyar tattaunawa ba tare da biyan kudin fansa ba.

To sai dai a bayanin shi, wakilin al’ummar Dan-Aji Malam Lawal Dogara ya shaida wa manema labarai cewa, bayan an hada wannan kudi ne suka wakilta Liman Malam Abdulkarim da Liman Babangida domin kai wadannan kudi domin a sako wadannan mata.

Gwamnatin Jihar ta Zamfara dai ta yi ta nuni da amso wadannan mata a matsayin gagarumar nasara da shirin da take yi na tattaunawa da ‘yan ta’adda ya haifar. To amma wannan bayani na mutanen Dan-Aji ya nuna idan har wancan shiri da Jihar Zamfara take yi yana da alfanu to bai shafi sako wadannan mata ba, duba ga bayanin dake cikin wannan video din.

Mu dai a nan jihar Katsina, duba ga irin cin amanar da suka yi mana cikin sulhun da mukayi dasu, muna nan kan matakin da muka dauka na yanke duk wata tattaunawa da ‘yan ta’adda har sai idan sun mika kawunan su tare da makaman su ga jami’an tsaro.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

Salihu Tanko Yakasai na hannunmu – DSS

Salihu Tanko Yakasai na hannunmu - DSS Rundunar 'yan sandan farin kaya ta DSS ta tabbatar da kama Salihu Tanko Yakasai, tsohon mai taimaka wa...

Ansako ɗaliban makarantar Kagara da aka sace

GSC Kagara: An sako mutum 41 da aka sace a makarantar Kagara ta Jihar Neja An sako ɗaliban makarantar Kagara da malamansu da ma'aikata guda...

PRESS RELEASE ; GANDUJE SACKS MEDIA AIDE

PRESS RELEASE GANDUJE SACKS MEDIA AIDE Governor Abdullahi Umar Ganduje of Kano state has relieved his Special Adviser on Media, Salihu Tanko Yakasai of his appointment...

KANO STATE POLICE COMMAND DIARY 26/02/2021

KANO STATE POLICE COMMAND DIARY 26/02/2021 7 DAYS ACHIEVEMENTS OF CP SAMA'ILA SHU'AIBU DIKKO, fsi IN KANO STATE ... As 9 Kidnapping Suspects, 8 Armed Robbery...

Bamu da Adalci, Dole ne mu cire batun Siyasa idan ba Haka ba Muna gidajenmu zamu Hallaka ~Inji Atiku Abubakar..

Bamu da Adalci, Dole ne mu cire batun Siyasa idan ba Haka ba Muna gidajenmu zamu Hallaka ~Inji Atiku Abubakar.. Tsohon mataimakin Shugaban Kasa Atiku...
%d bloggers like this: