CBN Ya Fitar Da Tsarin Gudanar Da Hada-hadar Kudade Ta Yanar Gizo

Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya fitar da sabon tsari wajen gudanar da hada-hadar kudade ta yanar gizo da kuma wasu wadanda suke da alaka da kimiyyar kudade. Babban Bankin ya bullo da wadannan tsarin ne domin magance matsalolin da ake samu wajen biyan kudi a cikin kasar nan.

“Tsarin zai taimaka wajen dai-daita harkokin kudade a Nijeriya da kara amfani da yanar gizo wajen hada-haadar kudade, inda a yanzu CBN ya samar da wani lambobin sirri wanda za a dunga amfani da shi wajen gudana da hada-hadar kudade a yanar gizo, domin gabatar da dangantaka a tsakanin abokanan huddar bankuna da ke cikin kasar nan.

“Tsarin ya kayyade yawan kudaden da za a gudanar da hada-hadar a yanar gizo, sannan ya samar da tsarin tabbatar da kulawa da hada-hadar kudade ta yanar gizo domin dakile ayyukan masu damfara a ta yanar gizo da kuma safarar kudade ba bisa ka’ida ba.

“Za a dunga samun rahoton hada-hadar kudade ta yanar gizo a sashin kula da tsarin biyan kudade da ke cikin babban bankin Nijeriya. Za a dunga kulawa da lamarin ne domin magance matsalolin damfarar kudade ta yanar gizo a cikin kasar nan.”

A cewar CBN, akwai lambobin sirri da aka samar wajen kulawa da hada-hadar gudanar da biyan kudade ta yanar gizo a Nijeriya domin kaucewa rashin garkiya.

Ya ce, an kuma kayyade yawan kudaden da za a dunga gudanar da hada-hadar ta yanar gizo a cikin kasar nan, wannan zai gudana ne bida ribar abokan kasuwancin bankuna. Ya ce, ana tsammanin kai mahimman rahoto game da duk wani rashin gaskiya, domin gudanar da bincike tare da daukan matakan da suka dace saboda hana faruwar lamarin a nan gaba.

“Kalmomin sirrin na biyan kudaden za su kasance ne bisa wasu kebabbun tsarin biyan kudade. Haka kuma bankin ya aiwatar da samar da wasu kalmomin sirri dai-daita tsaro cikin hada-hadar biyan kudade ta yanar gizo. Wannan zai gudana ne a tsakanin CBN da kuma kamfanoni,” in ji shi.

An dai shirya lambobin sirrin a na’urori ga masu amfani da hada-hada ta yanar gizo. Wannan lamari na samar da lambobin sirrin zai samar da ci gaba wajen biyan kudade a yanar gizo. A bangare daya kuma, zai rage tsohon hanyar da kamfanoni suke gwada kayayyakin da suka samar da ayyuka da kuma yadda suke gudanar da harkokin kasuwancinsu. Za a saka ido wajen kulawa da hanyoyin samarwa a tsakanin kamfanoni.

CBN ya bayyana cewa, yana kira ga ‘yan Nijeriya da su yi kokarin bin wannan tsari sau da kafa domin ci gaba da gudanar da gasa a tsakanin ‘yan kasuwa da yin amfani da na’urori na zamani wajen gudanar da hada-hadar kudade, domin hakan zai taimaka wajen bunkasa basirar abokanan kasuwanci a tsarin da suka dace.

Ya ci gaba da bayyana cewa, makasudin samar da wannan sabon tsarin dai shi ne, kara gudanar da harkokin kasuwanci ta hanayar kimiyya da fasaha da kara inganta ayyukan hada-hadar kudade da saukaka harkokin kudade a Nijeriya da kuma rage matsalar satar kudade ta yanar gizo.

Ya ce, bin wannan tsarin sau da kafa zai taimaka wajen inganta cibiyoyin kudade a Nijeriya da cike tazarar da ke tsakanin wadanda suka dade cikin lamarin da kuma masu tasowa a yanzu tare da samun alfanu mai yawan gaske. Ya ce, zai taimaka wajen samun ayyuka masu inganci ga abokan cinikayya wanda hakan zai rage hatsarin da suka dade suna fuskanta a baya.

Leadership Hausa

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here