Daga Usman Salisu Gurbin Mikiya

Wakilin Najeriya a Kasar Benin Laftanar-Janar Tukur Buratai Mai ritaya, yayi taro da Shugaban Kasar Jamhuriyar Benin Patrice Talon.

Buratai ya hadu da Shugaban ƙasar Benin a ranar Talata, a lokacin da ya gabatar da takardar kama aiki a Kasar.

Haka Zalika, Wakilin Kasar Germany a Jamhuriyar Benin Micheal Derus, gami da wakilan Kasashen Ghana da Gabon da Norway, suma sun gabatar da takardun su na kama aiki ga Shugaban Kasar Talon.

Taron Buratai da Shugaban ƙasar Benin na zuwane a dai-dai lokacin da ake kokarin maido da Dan Gwagwarmayar Kafa Kasar Yarbawa zalla, Sunday Adeyemo Wanda akafi sani da Sunday Igboho, da aka kama a Cotonou a ranar 19 ga watan Juli na Shekarar 2021, a lokacin da yake kokarin barin Kasar zuwa Germany.

Wani daga cikin makusancin Igboho Pelumi Olajengbesi yace, Buratai ya bukaci a maido da Igboho ga Sashen Kula da tsaro na Yansandan Farin Kaya na Nigeria amma Kasar Benin taki amincewa.

Buratai, Wanda ya kasance Shugaban Sojin Kasar Nigeria a tsakanin watan Juli na Shekarar 2015 zuwa watan Januri na Shekarar 2021, an kuma bashi Mukamin Wakilin Nigeria a Jamhuriyar Benin a watan yuni na Shekarar 2021.

Kafin wannan lokaci, Shugaban Ƙasar Nigeria Muhammadu Buhari ya gabatar da nadin sa, ga Majalisar Dattawa data Dokoki domin tabbatar da nadin shi, duk da koken da akeyi na rashin dai-dai a lokacin da yake Jagorantar Rundunar Sojin Kasar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here