Advert
Home Sashen Hausa Bukukuwan Mauludi a Katsina: ’YAN’UWA MUSULMI SUN YI FARETIN GIRMAMAWA GA ANNABI...

Bukukuwan Mauludi a Katsina: ’YAN’UWA MUSULMI SUN YI FARETIN GIRMAMAWA GA ANNABI (S).

Daga Bin Yaqoub Katsina

‘Yan’uwa Musulmi almajiran Shaikh ibraheem Zakzaky na da’irar Katsina sun shirya gagarumin taron faretin girmamawa ga Manzon Allah (S) wanda suka saba shiryawa duk shekara domin murna da zagayowar watan haihuwar Annabi (S).

Taron dai an fara shi ne misalin ƙarfe 12 na ranar yau Asabar 23/3/1443 (30/10/2021), a filin ATC cikin birnin Katsina. Kamar kowace shekara dai ana gabatar da gasar fareti ne tsakanin makarantun Islamiyoyyi da kuma Fudiyoyi da ke cikin garin. A bana ma an gabatar da gasar, sai dai kafin gasar a ɗabi’a akan baiwa Harisawa dama su fara gabatar da nasu faretin na share fage a matsayin iyaye.

Daga bisani Makarantun Fudiyoyi na firamare da sakandire su gabatar da nasu wanda duk ya ba ya daga cikin gasar, sannan sauran ‘yan gasa na makarantun Islamiyyu na dare su gwabza. A bana faretin ya kara ɗaukar sabon salo da zuwa da fasahohi gami da ƙir-ƙire-ƙir-ƙire.

Bayan gwabzawar dai makarantar Irshadu Subyan ta zo na 1 yayin da Tahriƙul Islam ta zo na 2 a guruf (A). A guruf (B) kuwa Fudiyya Islamiyya Shinkafi ce ta zo na ɗaya.

Wakilin ‘yan’uwa Musulmi na Katsina Shaikh Yaƙub Yahaya ne ya miƙa masu kyaututtuka tare da gabatar da jawabin rufewa. Shaihin Malamin dai ya iso muhallin ne ana gab da tashi taron, sai dai ya yi takaitaccen jawabi. In ba a manta ba Malamin Ya kawai tsawon wata biyu ba ya nan, yayin da ya tafi kasar waje neman lafiya.

Wannan ya sa filin taron ya kaure da sowwa gami da salati da kabbarori ya yin da ya isowwarsa wanda ya ke yau ne karon farko da ya bayyana a bainar jama’a tun bayan tafiyarsa.

KATSINA CITY NEWShttps://www.katsinacitynews.com
Danjuma Katsina, Dan Jarida, Manazarci, Marubuci, Mamallakin Jaridun KATSINA CITY NEWS, JARIDAR TASKAR LABARAI, THE LINKS NEWS, a karkashin Kamfanin MATASA MEDIA LINKS NIGERIAN LTD

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

THE FEDERAL MORTGAGE BANK OF NIGERIA (FMBN) HAS MADE HISTORY UNDER THE BUHARI ADMINISTRATION!

#PositiveFactsNG Do you know that ever since the Federal Mortgage Bank of Nigeria (FMBN) was established about 25 years ago, its greatest record of achievement...

YANZU-YANZU | Jirgin ruwan Bagwai dake jihar Kano mai dauke da fasinjoji 40 Yayi hatsari

Jirgin ruwan wanda ya debo dalibai mata da maza daga garin Badau zuwa garin Bagwai a jahar Kano yayi hatsari a cikin ruwan Yanzu...

ALLAH SARKI: ALLAH KA RABA MU DA RANAR NADAMA

Danjuma katsina  @Katsina City News A shekarar 2000 na dawo Katsina da zama, bayan shekaru na gwagwarmaya da tsallake siratsai kala-kala. Bayan na dawo na tsara...

Yadda Kotu Ta Ruguza Zaɓen Bangaren Ganduje Na Jam’iyyar APC

Wata babbar kotun Abuja ta soke zaben shugabannin jam'iyyar APC bangaren gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje. Alkalin kotun Hamza Muazu ya haramta zaben da...

EFCC Charges Corps Members To Take CDS More Seriously

The Port Harcourt Zonal Commander of the EFCC, Assistant Commander of the EFCC, ACE Aliyu Naibi has called on members of the National Youth...