Home Sashen Hausa BUKUKUWAN MAULUDI A ƘASASHEN MUSULMIN DUNIYA. Hotuna daga Isma'il Abubakar Idris katsina

BUKUKUWAN MAULUDI A ƘASASHEN MUSULMIN DUNIYA. Hotuna daga Isma’il Abubakar Idris katsina

BIKIN MAULUD A ƘASASHEN MUSULMIN DUNIYA.


Ranar 12 ga watan Rabi’u awwal na kowace shekara ranace da akasarin musulmin duniya (musamman ɗariƙun sufaye da shi’a mabiya iyalan gidan manzon Allah (S) suke fitowa ƙwansu da ƙwarƙatar su domin nunawa duniya farin ciki da samuwar manzon Allah s.a.w.


Kamar yanda tarihi ya nuna an haifi Annabi s.a.w Ranar 12 ga watan rabi’u awwal a garin Makka, a shekarar da ake kira da Shekarar Giwaye. Dalilin da ya sa ake kiran wannan shekara da haka kuwa shi ne wani gwamnan Sarkin Abbasiniya ne mai suna Abrahata ya shigo Makka da runduna mai yawa bisa giwaye (bayan ya kame garin Yaman) da nufin rusa Dakin Ka’aba da sauya alkiblar mutane zuwa San’a (domin a wancan lokacin mutane sukan kawo ziyarar bauta a Ka’aba) inda da ma tuni ya gina wani guri don wannan ziyara. Amma daga baya lokacin da Abrahata ya iso Makka da wannan runduna ta sa, sai Allah Ya aiko da wasu irin tsuntsaye dauke da tsakuwoyi a bakunansu, inda suka rinka jefo wadannan tsakuwoyi a kan wadannan runduna, nan take suka kashe sojojin da giwayen. Ta haka ne Allah Ya yi maganin wannan sarki da mutanen sa.

Mahaifinsa dai shi ne Abdullah dan Abdul Mutallibi dan Hashim; Mahaifiyarsa kuwa ita ce Amina ‘yar Wahbu, Kakansa kuwa shi ne Abdul Mutallibi, wanda ya kasance yana da ‘ya’yaye da yawa, amma Abdullahi (mahaifin Annabi) da Abu Talib (mahaifin sayyadi Ali) mahaifiyarsu guda ne. Don haka ya fito ne daga cikin madaukakin gidan nan na Bani Hashim wanda ya fito daga kabilar Kuraishawa wadanda ke da dangantaka da Annabi Isma’il (a.s) dan Annabi Ibrahim (a.s).

Manzon Allah (s) dai ya tashi ne a matsayin maraya saboda kasancewar mahaifinsa ya rasu yayin da ya kai ziyara Yathrib (Madina) watanni uku kafin haihuwar Manzon Allah (s). Tattare da bakin cikin rasuwar Abdullah, amma haihuwar wannan maraya(Manzon Allah s.a.w) ta sanya iyalansa, Amina da Abdul Mutallib, cikin farin ciki da ba shi da iyaka. Sun shirya gagarumar walima ga ‘yan’uwa da makwabta, inda aka yi yanka don murnar wannan haihuwa. A sakamakon haka duk Makka ta dauki murna, inda mutane suka yi ta zuwa gidan Abdul Mutallib don mika sakon taya murna gare shi.

l

Munfito ne domin nuna farinciki da haihuwar Annabi s.a.w wanda ya tsamar damu daga ɓata zuwa haske, kuma zanso inyi amfani da wan’nan dama da kuka bani, inyi kira ga duk wani mutum na duniya koma wane irin addini yake lallai yakamat ya fito ya nuna farincikin sa da samuwar wan’nan manzon, saboda shi Annabi nakowa ne ba ma musulmi ba kaɗai. Saboda shine wanda ya tsamar da duniya daga cikin duhun jahilci, domin shi muka san ilimin da muke rayuwa acikin sa. Cewar wani da KATSINA CITY NEWS ta zanta dashi.

Mun ɗauko maku Video da hotuna na yanda bukukuwan suka gudana, zamu sanya maku shi a Channel ɗin mu na YOUTUBE sai ku shiga ku ganewa idon ku dama sauran wasu bidiwoyin.


__________________________

KATSINA CITY NEWS Jarida ce dake busa yanar gizo akan www.katsinacitynews.com

Ko a YOUTUBE Channel ɗin mu dake KATSINA CITY NEWS.

Twitter:-@citynews

Facebookpage:-@KATSINACITYNWES

Instagram:-@katsinacitynews

Pinterest:-@katsinacitynews

Tumblr:-@Katsinacitynews

Telegram:-katsinacitynews

LinkedIn:-katsinacitynews

Advertisement:GREENTIDE AGRO
Advertisement:-GREENTIDE AGRO

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

Salihu Tanko Yakasai na hannunmu – DSS

Salihu Tanko Yakasai na hannunmu - DSS Rundunar 'yan sandan farin kaya ta DSS ta tabbatar da kama Salihu Tanko Yakasai, tsohon mai taimaka wa...

Ansako ɗaliban makarantar Kagara da aka sace

GSC Kagara: An sako mutum 41 da aka sace a makarantar Kagara ta Jihar Neja An sako ɗaliban makarantar Kagara da malamansu da ma'aikata guda...

PRESS RELEASE ; GANDUJE SACKS MEDIA AIDE

PRESS RELEASE GANDUJE SACKS MEDIA AIDE Governor Abdullahi Umar Ganduje of Kano state has relieved his Special Adviser on Media, Salihu Tanko Yakasai of his appointment...

KANO STATE POLICE COMMAND DIARY 26/02/2021

KANO STATE POLICE COMMAND DIARY 26/02/2021 7 DAYS ACHIEVEMENTS OF CP SAMA'ILA SHU'AIBU DIKKO, fsi IN KANO STATE ... As 9 Kidnapping Suspects, 8 Armed Robbery...

Bamu da Adalci, Dole ne mu cire batun Siyasa idan ba Haka ba Muna gidajenmu zamu Hallaka ~Inji Atiku Abubakar..

Bamu da Adalci, Dole ne mu cire batun Siyasa idan ba Haka ba Muna gidajenmu zamu Hallaka ~Inji Atiku Abubakar.. Tsohon mataimakin Shugaban Kasa Atiku...
%d bloggers like this: