A baya ya fuskanci shari’a bisa zargin kin bayyana kaddarorinsa amma Kotun Kolin Najeriya ta wanke shi a shekara ta 2018

Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya ta’annati, EFCC, ta ce ta tsare tsohon shugaban majalisar dattawan kasar, Sanata Bukola Saraki.

Mai magana da yawun EFCC, Wilson Uwujaren, ya tabbatar wa BBC ranar Asabar cewa sun gayyaci Sanata Saraki ne domin ya amsa wasu tambayoyi game da zarge-zargen cin hanci.

Sai dai bai yi cikakken bayani kan zarge-zargen da suke yi wa tsohon gwamnan jihar ta Kwara ba.

Sanata Saraki, wanda ya shafe shekaru takwas a matsayin gwamnan jihar Kwara, ya daɗe yana fuskantar zargin cin hanci da kuma halatta kudin haramun.

A baya ya fuskanci shari’a bisa zargin kin bayyana kaddarorinsa amma Kotun Kolin Najeriya ta wanke shi a shekara ta 2018.

A 2019, EFCC ta garkame gidaje akalla biyar na Sanata Saraki da ke jihar Lagos bayan ta yi zargin cewa ya mallake su “ta hanyar wawure baitul malin jihar Kwara domin azurta kansa.”

A lokacin da yake shugabancin majalisar dattawa, an sha kai ruwa rana tsakaninsa da na bangaren zartarwa karkashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here