Buhari zai yi wa ƴan Najeriya jawabin sabuwar shekara gobe Juma’a

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai yi wa ƙasar jawabin sabuwar shekara a gobe ɗaya ga watan Janairun 2021.
Mai taimaka wa shugaban kan kafofin watsa labarai Malam Garba Shehu ne ya sanar da hakan a shafinsa na Twitter inda ya ce shugaban zai yi jawabin ne da misalin ƙarfe 7:00 na safe.
Malam Garba Shehu, ya buƙaci kafafen watsa labarai na rediyo da talabijin da su jona da gidan talabijin na ƙasar wato NTA da kuma gidan rediyo na tarayya FRCN domin su ma su yaɗa jawabin na shugaban kasar.