SHUGABA BUHARI YA AIKE DA TA’AZIYYA GA RUNDUNAR SOJIN SAMA IYALAN DA SUKA RASA RAYUKAN SU CIKIN HATSARIN JIRGI

Fassara: Hon. Buhari Sallau Hadimin Shugaban kasa Muhammadu Buhari Bangaren Rediyo da Talabijin.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana bakin cikin sa kan hatsarin jirgin saman rundunar sojin saman najeriya na (NAF) Beechcraft KingAir B350i a ranan lahadi a birnin Abuja kanda wannan hatsari yaci rayukan mutane bakwai ma’aikata.

Amadadin gwamnatin tarayya, Shugaba Buhari yana kara aikewa da ta’aziyya zuwa ga membobin iyalai, abokai, da kuma abokan aiki na wainnan mutane da suka rasa rayukan su a sakamakon wannan bala’i.

Shugaban kasa ya bi sahun rundunar sojin saman najeriya, rundunar soji da kuma sauran yan najeriya cikin bakin ciki na wannan rashi kuma abun bakin ciki wanda suka sadaukar kuma suka karfafa ma’aikata, wainda suka rasu cikin hanyan gudanar da aiki.

Shugaba Buhari ya lura da cewa a gudanar da bincike kan dalilin da ya haifar da wannan hatsarin yana tafiya, domun kuwa kare sararin saman najeriya zai ci gaba da zama muhimmi ne ga gwamnati

Yayi Addu’a zuwa ga Allah ya bada hakuri wa iyalan da ke wannan makokin da kuma kasa baki daya kuma ka baiwa wannan rayuka sa’an tashi cikin kwanciyar hankali.

Femi Adesina:
Babban Mai bawa Shugaban kasa shawara kan kafofin watsa labarai da wayar da kan jama’a
21, ga watan fabrairu na shekarar 2021.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here