Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana alhininsa kan kisan gilla da aka yi wa manoma 45 tare da raunata wasu da dama sakamakon sabon tashin hankali a kananan hukumomin Lafia, Obi da Awe na jihar Nasarawa.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakain shugaban ya fitar Malam Garba Shehu.

Shugaba Buhari ya ce al’ummar kasar baki daya sun tausayawa iyalan wadanda abin ya shafa.

“Ina tabbatar wa jama’a da gaske da kuma cewa wannan gwamnati tana yin iya kokarinta wajen ganin ta kare lafiyar jama’a kuma ba za tai sakaci ba wajen kamo wadanda suka aikata wannan ta’asa ta rashin hankali da dabbanci, tare da gurfanar da su a gaban kuliya,” inji shi. .

Ya kuma jajantawa gwamnati da al’ummar jihar, ya kuma nuna jin dadinsa da yadda gwamnatin jihar ta dauki matakin gaggawa kan lamarin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here