Buhari ya yi farin cikin dawowar ɗaliban Jangebe

PRESIDENCY

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nuna farin cikin game da sakin daliban nan mata da aka sace a jihar Zamfara.

Cikin wata sanarwa da mataimaki na musamman ga shugaban kan harkokin yada labarai Garba Shehu ya fitar , Buhari ya ce, “Zan shiga sahun iyalin da mutanen Zamfara na taya daliban da aka sace murnanr dawowa gida.”

Shugaba Buhari ya kara da cewa ya yi murnar dawowar daliban gida ba tare da wata cutuwa ba, ya kara da cewa “tsare mutum ba karamin tashin hankali ba ne ba kawai ga wadanda aka kama ba, har ga iyalansu da kuma mu ba ki daya.”

Buhari ya yi kira ga mutane da su zama masu sanya idanu kan yankunan da suke tare da bayar da cikakken hadin kai ga jami’an tsaro domin dakile hare-haren barayin dajin da wuri.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here