Home Sashen Hausa Buhari ya yi Allah wadai da kisan mutane 70 a Jamhuriyyar Nijar

Buhari ya yi Allah wadai da kisan mutane 70 a Jamhuriyyar Nijar

Buhari ya yi Allah wadai da kisan mutane 70 a Jamhuriyyar Nijar

Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya yi Allah wadai da kisan mutane 70 a garin Zaroumdareye, wani gari da ke kan iyaka tsakanin Jamhuriyar Nijar da Mali da ‘yan ta-da-kayar baya suka yi, ya na mai bayyana lamarin da cewa wani kira ne na ganin an hada karfi da karfe don magance ta’addanci.

Shugaba Buhari ya ce, “Na yi matukar kaduwa da kisan mutane da dama marasa laifi” da wadannan mugayen tsageru suka yi.

A cewar Shugaban, “Muna fuskantar babban ƙalubale na tsaro saboda yaƙin da ake yi da ƴan ta’adda a yankin Sahel kuma daukar matakan hadin kai ne kawai zai taimaka mana wajen fatattakar wadannan muggan makiya jama’a”.

Ya bayyana cewa “ta’addanci yanzu ya zama kamar wata muguwar cuta wacce ke iya yaduwa a kowane lokaci matukar ba a dauki mataki na bai daya ba.”

Shugaba Buhari ya ce “rashin zaman lafiya a wani yanki na Afirka na da tasiri ga tsaron wasu wasu ƙasashen.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

YANDA ZAMAN KOTUN MAHADI SHEHU DA MUSTAFA INUWA YA GUDANA A BABBAR KOTUN DUTSIN-MA

YANDA ZAMAN KOTUN MAHADI SHEHU DA MUSTAFA INUWA YA GUDANA A BABBAR KOTUN DUTSIN-MA Da misalin karfe 10:20 na safiyar yau Litinin, Alkalai uku sun...

PRESIDENT BUHARI RECEIVES FMR VP ARCH NAMADI SAMBO ON NIGER ELECTION.

PRESIDENT BUHARI RECEIVES FMR VP ARCH NAMADI SAMBO ON NIGER ELECTION. President Muhammadu Buhari receives the Former Vice President Arch Namadi Sambo on the Republic...

WACCE KOTU ZA A KAI MAHADI SHEHU GOBE?

WACCE KOTU ZA A KAI MAHADI SHEHU GOBE? muazu hassan @ jaridar taskar labarai Gobe za a kai mahadi shehu Wanda yan sanda suka kawo daga Abuja...

Group Seek To End Discrimination, Call For Unity

Group Seek To End Discrimination, Call For Unity By Bello Hamza, Abuja The group under the aegis of initiative for coalition and rights protection a not...
%d bloggers like this: