Majalisar kolin kasa (masu mulki da tsaffin shugabanni) ta yafewa tsohon gwamnan jihar Taraba, Jolly Nyame da tsohon gwamnan Plateau, Joshua Dariye, dake garkame a kurkuku bisa laifukan satar dukiyar al’umma.

Gwamnonin biyu na cikin fursunoni 159 da majalisar ta yafewa karkashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari ranar Alhamis a birnin tarayya Abuja.

Daga cikin wadanda aka yafewa tsohon soja da minista lokacin Abacha, Tajudeen Olanrewaju; Laftanan Kanar Akiyode, da dukkan Sojojin da aka daure kan laifin hannun cikin yunkurin juyin mulkin Gideon Orkar a 1990.

A cewar wata majiya daga fadar shugaban kasa, an yafewa tsaffin gwamnonin biyu ne bisa lafiya da yawan shekarunsu.

Jolly Nyame, wanda tsohon gwamnan Taraba ne tsakanin 1999 da 2007, na zaman shekaru 12 da kotu ta yanke masa a Kurkukun Kuje kan laifin almundahanar dukiyar jama’a.

Shi kuma Joshua Dariya, wanda tsohon Gwamnan Plateau ne tsakanin 1999 da 2007, na zaman kurkuku ne kan laifin satan N2bn na kudin jama’arsa.

Kotu ta yanke masa hukunci a Yunin 2018, lokacin yana ofis matsayin Sanata mai wakiltan Plateau ta tsakiya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here