Buhari ya tafi Daura
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sauka cibiyarsa Daura a jihar Katsina kamar yadda fadarsa taBAYYANA
Gwamnan Katsina Aminu Bello Masari da mataimakinsa Mannir Yakubu da sauran maƙaraban gwamnati da shugabannin Jami’an tsaro ne suka tarbi shugaban a Katsina bayan saukarsa jirgi da yamma, kamar yadda sanarwar da fadar shugaban ta bayyana.
Ya kuma samu tarba daga Mai Martaba Sarkin Daura Alhaji Umar Faruk da sauran majalisar sarakuna ta jihar Katsina inda aka yi masa ƴar ƙaramar daba.
Sarkin Daura kuma ya ba shugaba Buhari kyautar doki da takobi a matsayinsa na Bayajiddan Daura.
Sanarwar da Malam Garba Shehu ya fitar ta ce suna sa ran daga can shugaban zai shiga taron majalisar zartarwa a ranar Larabawa ta Intanet.