#GaskiyarLamarinNijeriya

Ko kun san cewa, Gwamnatin Shugaba Buhari ta samar da sababbin motoci masu fasahar tsaro na musamman guda shida, don sa idanu kan zirga-zirgar jiragen ƙasa daga Abuja zuwa Kaduna?

An yi wa motocin ƙira ta musamman tare da fasahar zamani, wacce za su riƙa tura wa da bayanai nan take duk minti guda, don tabbatar da cewa, komai na tafiya daidai a kan layin dogon da kuma hanyar bakiɗaya.

Wannan na daga cikin namijin ƙoƙarin da Gwamnatin Shugaba Buhari ke yi wajen ganin ta kawo ƙarshen matsalolin tsaro da suka addabi hanyar Abuja zuwa Kaduna a kwanan nan!