Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya kaddamar da motocin aiki kirar Buffalo sama da 200 da sauran kayayyakin tsaro da gwamnatin tarayya ta siyo ta hannun Asusun ‘Yan sandan Najeriya (NPTF), ga ‘yan sandan Najeriya.

Da ya ke kaddamar da motocin da sauran kayayyakin tsaro a Abuja, Buhari ya bayyana samar da kayayyakin a matsayin wani bangare na sake fasalin rundunar ‘yan sandan Najeriya.

Shugaban wanda ya samu wakilcin ministan harkokin ‘yan sanda, Alhaji Muhammad Dingyadi, ya bayyana cewa shirin na taimakawa ‘yan sanda a Najeriya, ta hanyar samar da ababen more rayuwa na zamani.

Buhari ya yabawa kwamitin amintattu, gudanarwa da ma’aikatan NPTF bisa yadda suka kamalla ayyukan da suka yi da kyau, wanda ya nuna an fara kaddamar da ayyuka da dama.

Ya ce, horarwa da zamanantar da kayayyakin aikin ‘yan sanda, sun kasance daidai da umarnin Gwamnatin Tarayya na zurfafa tsaro a fadin kasar

Source: PlatinumPost

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here