Buhari ya gaza kawai ya sauka daga shugabancin Najeriya’
A Najeriya, masu sharhi sun fara bayyana ra’ayinsu kan yadda matsalar tsaro ke ci gaba da haukata a arewacin ƙasar, inda yanzu haka ake zaman makoki, bayan mummunan kisan gillar da Boko Haram ta yi wa gomman manoma a jihar Borno cikin ƙarshen mako.
Har yanzu dai ana neman wasu daga cikin mutanen da harin ya ritsa da su, yayin da wasu ‘yan Najeriya ke ganin ko shugaba Muhammadu Buhari ya tashi tsaye wajen magance matsalar, ko kuma ya sauka daga mulki.
Kabiru Dakata na daga cikin masu ririn wannan ra’ayi kamar yadda za a iya ji a rahoton AbdusSalam Ibrahim Ahmed: