Buhari ya amince a kafa sabbin jami’o’i biyar

Muhammadu Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya Amince da kafa wasu sabbin jami’o’in fasaha da na lafiya guda 5 da zummar ganin an kawo karshen kalubalen da ake fuskanta na karancin likitoci a kasar.

Ya kuma amince da bayar da tallafin Naira Biliyan 4 ga kowacce daga cikin jami’o’in fasahar biyu da za a samar, da kuma Naira Biliyan biyar ga na koyar da harkokin kiwon lafiya.

Za a basu wadannan kuae ne daga asusun bada tallafi na TETFund,.

Jaridar Daily Trust ta rawaito babban Sakatare a ma’aikatar Ilimi ta Najeriya Sonny Echono na bayyana cewa za a samar da jami’o’in Fasaha biyu a jihohin Jigawa da Akwa Ibom, yayin da kuma za a kafa na koyar da hakokin kiwon lafiya a Azare dake Jihar Bauchi da Ila Orangun, a Jihar Osun.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here