Buhari ya amince a kafa hukumar takaita yaduwar kananan makamai

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya amince a kafa hukumar takaita yaduwar kananan makamai a kasar.

Sanarwar da mai taimaka wa shugaban kasar kan shafukan sada zumunta, Bashir Ahmad, ya wallafa a shafinsa na Twitter ranar Litinin, ya ambato mai magana da yawun ofishin mai ba Buhari shawara kan sha’anin tsaro yana cewa hukumar za ta kasance a ofishin nasu.

Hukumar za ta maye gurbin kwamitin shugaban kasa kan dakile yaduwar kananan makamai, in ji sanarwar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here