Buhari ya amince a gina sabon asibiti a fadar shugabn ƙasa
Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya amince da gina sabon asibitin sha-ka-tafi a fadar shugaban ƙasa mai gado 14, a cewar rahoton Daily Trust.

An tsara za a gina asibitin kan kuɗi naira biliyan 21.9 wanda kamfanin Julius Berger Nigeria Limited zai fara aikin sa daga ranar Litinin, kamar yadda sakataren fadar, Umar Tijjani, ya bayyana wa wani kwamatin Majalisar Dattawa.

Sai dai har yanzu majalisar ba ta kammala duba kasafin kuɗin 2022 ba kafin ta amince da shi, wanda a ciki ne gwamnatin Buhari ta ware kuɗin gina asibitin.

Mista Tijjani ya ce za a kammala aikin a Disamban 2022.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here