Ko kun san cewa, a ranar Alhamis, 9 ga Disamba, 2021, Shugaba Muhammadu Buhari ya ƙaddamar da sashen kashu uku na aikin titin Kano zuwa Maiduguri mai tsawon kilomita 106.341, wanda ya haɗa Azare zuwa Potiskum a jihohin Bauchi da Yobe?

Shugaba Buhari, wanda Ƙaramar Ministar Masana’antu, Kasuwanci da Zuba Jari, Jakada Maryam Yalwaji-Katagum, ta wakilta, ya bayyana yadda kammala titin zai bunƙasa harkokin kasuwanci da samar da aikin yi ga ɗimbin mutane, domin tsamo su daga ƙangin talauci.

Tun asali dai an bayar da aikin sashen titin ne kan kuɗi Naira Biliyan 29.1 a shekara ta 2006da nufin kammala shi a 2010, to amma daga bisani aka ƙara kuɗin zuwa Naira Biliyan 45.81, inda za a kammala cikin watanni 42.

Titin ya ƙunshi tsawon kilomita 93.2 daga Azare zuwa Potiskum da kilomita 1.17 na mahaɗar Azare, kilomita 10.5 na ratsen bayan garin Potiskum, kilomita 1.936 na hannu ɗaya da gadoji uku da sauransu, inda aka amince da kammala aikin zuwa watan Nuwamba na 2021.

Yanzu tirin ya haɗa manyan garuruwa kamar Katagum da Dambam a Jihar Bauchi da ƙananan hukumomin Nangere da Potiskum a Jihar Yobe State.

Ita kanta Gwamnatin Jihar Bauchi ta gode wa Gwamnatin Shugaba Buhari bisa kammala wannan aiki mai matuƙar muhimmanci, wanda ya gagari gwamnatocin baya, sannan ta gode wa Shugaba Buhari bisa amincewa da aikin faɗaɗa titin Bauchi zuwa Kano da kuma Bauchi zuwa Maiduguri, baya ga aikin titi mai tsawon kilomita 82, wanda ya tashi daga Alƙaleri zuwa Futuk da ya haɗe jihohin Bauchi da Gombe, duka a ƙarƙashin jagorancin Shugaba Buhari.

Wannan ya gwada yadda Gwamnatin Tarayya a ƙarƙashin jagorancin Muhammadu Buhari ta ke aiwatar da muhimman ayyuka, domin kyautata rayuwar al’ummar Nijeriya!

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here