Advert
Home Sashen Hausa Buhari da Zulum na alhinin rasuwar sojojin Najeriya

Buhari da Zulum na alhinin rasuwar sojojin Najeriya

Buhari da Zulum na alhinin rasuwar sojojin Najeriya

Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da Gwamnan Jihar Borno Babagana Umara Zulum na alhinin rasuwar Birgediya Janar Dzarma Zirkusu da mayaƙan ISWAP suka kashe ranar Asabar.

Shugaban ya ce ransa “ya ɓaci matuƙa” da samun labarin rasuwar janar ɗin da kuma wasu soja uku da ‘yan bindigar suka yi wa kwanton-ɓauna a garin Askira Uba na Jihar Borno.

“Ban ji daɗin labarin rasuwar Janar Dzarma Zirkusu ba da kuma soja uku da suka sadaukar da ransu. Najeriya ta yi rashin jajirtattu. Na jinjina wa ƙoƙarinsu. Allah ya ji ƙan su,” a cewar Buhari cikin wata sanarwa daga fadarsa.

A gefe guda, shi ma Gwamna Zulum ya miƙa ta’aziyyarsa ga rundunar sojan Najeriya, yana mai gode wa dukkanin dakarun bisa abin da ya kira “sadaukarwar da suka yi wa Najeriya”.

Zulum

Dakarun na sojan Najeriya sun rasu ne yayin da suke kan hanyar kai wa ‘yan uwansu ɗauki sakamakon harin da mayaƙan ƙungiyar ISWAP mai iƙirarin jihadi ta kai wa sansaninsu na Askira Uba.

Sojojin sun kashe ‘yan bindigar da dama tare da lalata kayan yaƙinsu a fafatawar, a cewar rundunar.

KATSINA CITY NEWShttps://www.katsinacitynews.com
Danjuma Katsina, Dan Jarida, Manazarci, Marubuci, Mamallakin Jaridun KATSINA CITY NEWS, JARIDAR TASKAR LABARAI, THE LINKS NEWS, a karkashin Kamfanin MATASA MEDIA LINKS NIGERIAN LTD

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

THE FEDERAL MORTGAGE BANK OF NIGERIA (FMBN) HAS MADE HISTORY UNDER THE BUHARI ADMINISTRATION!

#PositiveFactsNG Do you know that ever since the Federal Mortgage Bank of Nigeria (FMBN) was established about 25 years ago, its greatest record of achievement...

YANZU-YANZU | Jirgin ruwan Bagwai dake jihar Kano mai dauke da fasinjoji 40 Yayi hatsari

Jirgin ruwan wanda ya debo dalibai mata da maza daga garin Badau zuwa garin Bagwai a jahar Kano yayi hatsari a cikin ruwan Yanzu...

ALLAH SARKI: ALLAH KA RABA MU DA RANAR NADAMA

Danjuma katsina  @Katsina City News A shekarar 2000 na dawo Katsina da zama, bayan shekaru na gwagwarmaya da tsallake siratsai kala-kala. Bayan na dawo na tsara...

Yadda Kotu Ta Ruguza Zaɓen Bangaren Ganduje Na Jam’iyyar APC

Wata babbar kotun Abuja ta soke zaben shugabannin jam'iyyar APC bangaren gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje. Alkalin kotun Hamza Muazu ya haramta zaben da...

EFCC Charges Corps Members To Take CDS More Seriously

The Port Harcourt Zonal Commander of the EFCC, Assistant Commander of the EFCC, ACE Aliyu Naibi has called on members of the National Youth...