Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabi’u Kwankwaso, ya ce Shugaban kasa, Manjo Janar Muhammadu Buhari (mai ritaya), ba zai sanya hannu kan dokar zabe kato bayan kato ba, domin gwamnonin sun matsa masa lamba kan kada ya amince.

Kwankwaso ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da jaridar The PUNCH gabanin hutun majalisar dokokin kasar.

Tsohon gwamnan ya ce, hakika, zaben fidda gwanin kai tsaye na tilas zai samar da daidaito da kuma tabbatar da cewa ’yan takara masu farin jini sun fito.

Sai dai ya ce saboda irin wannan fidda gwani na tilas na iya sa gwamnoni su yi kasa a gwiwa, ba za su goyi bayan hakan ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here