Advert
Home Sashen Hausa BUDADDIYAR WASIKA ZUWA GA MALAM SHITTU S SHITTU

BUDADDIYAR WASIKA ZUWA GA MALAM SHITTU S SHITTU

Mai girma Shugaban Riko na Jam’iyyar APC.

Mun rubuto maka wannan wasika ne a matsayinmu na ‘yan kungiyar Gamayyar Kungiyoyin Jam’iyyar APC na Jihar Katsina.

Muna son tunawa da jawo hankalinka a kan irin gata da biyayya da Bala Abu Musawa ya yi maka.

Da farko kana Kakakin Jam’iyya mukami na kusan karshe a APC ya mara maka baya aka ba ka Shugaban Riko, shi ne na farko da ya yi maka bai’a, kuma ya shelanta cewa ya ji, ya kuma bi a gaban kowa.

Da aka zo zabe, shi ne ya sake mara maka baya aka zabe ka aka zabe ku tare, ya kuma ci gaba da yi maka biyayya.

Da aka rusa ku, aka ba ku riko, yana cikin na gaba-gaba wajen yi maka da’a.

Kai ka sani iyakar sani, a shekarun da kuka yi kuna shugabanci, yana gaba-gaba wajen kare martabar Jam’iyya da kuma kai.

Ko taro aka je, ka fi natsuwa Bala Abu ya yi magana. Duk wani taron Jam’iyya in ba ka ba shi umurni ba, ba ya zuwa.

Yana da halin shiga ko’ina, amma har wajen Gwamna ba ka taba kama shi da yi maka zagon kasa, ko cin dunduniya ba.

Tun da yanzu ta tabbata bisa tsarin Abuja kai ba za ka yi takara ba, abin da ya kamata shi ne ka mara wa Bala Abu Musawa baya ya zama Shugaban APC.

Wannan sh ine zai nuna ka martaba da mutunta yi maka biyayya da ya yi a baya. Domin Hausawa na cewa;
“Yaba kyauta tukwuici”.

Sako daga
Gamayyar Kungiyoyin jam’iyyar APC a Jihar Katsina

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

ADMISSION FORM IS AVAILABLE @ SILICON HEIGHT INTERNATIONAL COLLEGE KATSINA.

SILICON HEIGHT INTERNATIONAL, SCHOOL WISHES TO INFORM THE GENERAL PUBLIC THAT,THE SALE OF FORMS INTO NURSERY, PRIMARY AND SECONDARY IS STILL ONGOING. THE SCHOOL...

Gwamna Aminu Bello Masari ya buɗe taron shuwagabannin Majalisun jihohin Najeriya a Katsina…

Mai girma Gwamnan Jihar Katsina ya bude taron shugabannin majalisun Dokokin Jihohin Najeriya (36) a kwata na uku, da Jihar ta dauki bakunci. Taron da...

Jihar Katsina ta amshi bakuncin Kakakin majalisun Dokokin Jihohin kasar (36).

A cikin shirye, shiryen gudanar da Babban taron Kungiyar wanda ta sabayi lokaci bayan lokaci, domin tattauna al'amurran da suka shafi kasa. Taken taron na...
%d bloggers like this: