BUDADDIYAR WASIKA ZUWA GA MAI GIRMA GWAMNAN KATSINA Rt. HON AMINU BELLO MASARI

Mai girma Gwamna kamar yanda ka sani, na sheda maka da kaina a rubuce mae kuma sheda maka baki da baki cewa kai a matsayin uba nike kallon ka duk da kasancewar ban taba uba a siyasa ba. Tabbas tunda Allah yasa na shiga siyasa ba a taba mutumen da ya karrama ni ba, ya mutunta ni kuma yayi mani taimako irin ka ba. Ina son duniya ta sani ban taba neman taimako ba wajen ka ya mai girma Gwamna wanda baka yi mani shiba. Ka taimake ni matuka kuma ina godiya maras adadi.

Ya mai girma Gwamna zan tuna maka a ranar da na dawo APC dani da kai da Alhaji Dahiru munyi maganar AMANA wanda har na tambaye ka ni tawa amanar a hannun wa take kace tana hannun ka da Alhaji Dahiru wanda a nan na daga hannu nace Allah kana shaida kuma daga nan bamu kara magana a kan komai ba. Allah ya sani a bisa wannan amanar nike har ya zuwa yau kuma babu abinda ba zan iya yi ba don tabbatar da ita har sai in ka saba.

Za kayi mamakin bin wannan hanyar domin isar da wannan sako a gare ka kasancewar bani da shamaki da kai kamar yanda nima nayi mamakin yanda yaron ka, dan majalisar Dutsinma, Malam Muhammadu Hamisu yayi rubutu a bisa umurnin ka, kamar yanda yake fadi ma mutane, yaci mani mutunci dani da sauran mutanen da muke cikin kungiyar HESDIN duk da kasancewar kana iya kira na kuma inzo. A tunani na, a bisa amana in har akwai kuskuren da nayi a cikin wannan aiki na kungiyar tsaro ta Dutsinma, to kamata yayi ka sa a kira ni ka nuna mani laifi na ba a ci mani mutunci ba a idon duniya. Ba haka amana tace ba.

Mai girma Gwamna naji labarin zaka shigo Dutsinma gobe Talata, kamar yanda ake fada, domin ka gaya ma mutanen Dutsinma cewa, cin mutuncin da dan majalisa yayi mamu kai kasa shi don ka fitar dashi daga fushin al’umma da zargi. Wannan magana in har gaskiya ce, abinda kuma nike zaton ba haka bane, to har ga Allah ba a taba Gwamna irinka ba. Duk wani uzuri da muke baka da wani suka da akeyi ma jami’an ka tabbas ta tabbata alhakin su kawai al’umma ke dauka da sanin ka ake komai.

Mu kuma a Dutsinma in har haka ta kasance to babu tantama bamu san ciwon kan mu ba. Ya mai girma Gwamna ko ka san Mutum nawa ya zuwa yau aka kashe a Dutsinma sanadiyyar banditry? Mai girma Gwamna ko ka san Mutum nawa suka tsiyace sanadiyyar biyan kudin fansa a Dutsinma? Mai girma Gwamna ko ka san Mutum nawa ne ke kwana a kan icce in dare yayi saboda yafi sauki su kwana a kan icce than kan katifar gidajen su saboda matsalar tsaro a Dutsinma? Mai girma Gwamna ko ka san cewa akwai Mutum 13 da aka dauke Shekaranjiya daga sanawa kudin fansar su ake nema, aka kwashe dukuyoyin jama’ar gari, a ka kona shaguna wanda wasunsu sun tsiyace kenan har abada? Ya mai girma Gwamna ko ka san shekaranjiya a Fararu barayi sun bi gida gida duk sun kore masu shanu kuma iyakar maganar kenan?

Yanzun mai girma Gwamna bacin baka taba zuwa mamu jaje ba, baka taba aikowa ba yanzun mai girma Gwamna sai a kan dan majalisa zaka zo Dutsinma? Allah ya sawwake.

Ban isa in hana ka ba amman dai ayi shawara don Allah.

Mai biyayya kamar kullum a gareka Umar Tata.
MUN KWAFO DAGA SHAFIN UMAR TATA NA FACEBOOK

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here