Buba Marwa ya ce mutum miliyan 15 ke tu’ammuli da kwaya a Najeriya

Tsohon gwamnan Legas Birgediya Janar Buba Marwa ya fara aiki a matsayin sabon shugaban hukumar da ke yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta NDLEA a Najeriya.

A lokacin da yake gabatar da jawabin farko a hedikwatar NDLEA a Abuja, Buba Marwa ya bayyana damuwa kan ƙaruwar yawan masu amfani da miyagun ƙwayoyi inda ya ce a 2018 an gano kimanin ƴan Najeriya miliyan 14.3 ke tu’ammuli da miyagun ƙwayoyi.

Kuma a cewarsa yawancinsu ƴan tsakanin shekara 15 ne zuwa 64.

Tsohon gwamnan soja na Legas da Borno ya sha alwashin tabbatar da gyara tare da faɗaɗa ayyukan hukumar NDLEA.

Ya ce, hukumar za ta yi ƙoƙari ƙarƙashin jagorancin shi domin rage yawan tu’ammuli da ƙwayoyi sannan ya yi alƙwalin inganta rayuwar ma’aikatan hukumar.

Social embed from twitter

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here