Home Sashen Hausa Boko Haram ta kashe masu faskare uku, ta kama 40 a Borno

Boko Haram ta kashe masu faskare uku, ta kama 40 a Borno

Boko Haram ta kashe masu faskare uku, ta kama 40 a Borno

Mayaƙa masu iƙirarin jihadi a Najeriya

Wasu da ake zargin ‘yan Boko Haram ne sun kashe masu saran itace uku, sun kuma sace wasu kimanin 40 a Jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya.

Jami’an sa-kai a yankin sun faɗa wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa an yi wa masu saran itacen tsinke ne a dajin Wulgo da ke kusa da kan iyakar Kamaru.

Da ma dai yankin sananne ne wajen ayyukan ‘yan ta-da-ƙayar-bayan, inda suke da sansanoni da yawa.

Masu faskaren sun je dajin Wulgo ne don neman itace amma ba su dawo ba har maraiace, abin da ya sa ‘yan gora suka bi bayansu, sai dai ba su ga kowa ba sai gawa uku da aka harba a baya.

“Ga dukkan alamu, duka mutum ukun an harbe su ne bayan sun yi yunƙurin tserewa saboda dakkansu an harbe su a baya,” a cewar wani shugaban ƙungiyar ‘yan gora a yankin.

An shafe tsawon lokaci babu layin salula a yankin sakamakon hare-haren da Boko Haram ta riƙa kaiwa tare da karya turakun layukan. Hakan ya tilasta wa mazauna yankin amfani da layukan Kamaru.

Mayaƙan Boko Haram na ƙara far wa masu saran itace da manoma, bisa zargin suna bai wa sojoji da ‘yan gora bayanai.

Hukumomi na gargaɗin masu faskare su guji shiga daji, sai dai rahotanni na cewa tilas ce ke sanya su yin hakan saboda an sare tsirrai a yankunan da ke da zaman lafiya.

Bayanan bidiyo,Bidiyo: Abin da BBC Hausa ta gano da ta je Zabarmari

Rikicin Boko Haram ya yi sanadiyyar mutuwar mutum fiye da 36,000 tare da raba sama da miliyan ɗaya da mahallansu, a cewar Majalisar Ɗinkin Duniya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

Sake Gina Hanyar Katsina zuwa Kano: Ministan Ayyuka Mr. Fashola yace ana gab da kammala Aikin hanyar.

Sake Gina Hanyar Katsina zuwa Kano: Ministan Ayyuka Mr. Fashola yace ana gab da kammala Aikin hanyar. Ministan ya bayyana haka ne bayan zaman Majalisar...

An sanya dokar hana fita a garin Jangebe na Zamfara

An sanya dokar hana fita a garin Jangebe na Zamfara Gwamnatin jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya ta sanya dokar hana fita a garin Jangebe...

Jama’atu Nasril Islam tace bazata Shiga Mahawar da Gwamnatin Jihar Kano ta shirya tsakanin Sheikh Abduljabbar da Maluman Kano ba….

Jama'atu Nasril Islam tace bazata Shiga Mahawar da Gwamnatin Jihar Kano ta shirya tsakanin Sheikh Abduljabbar da Maluman Kano ba.... A wata Sanarwa da Sakataren...

Yanzu-yanzu: Buhari ya bada umurnin a bindige duk wanda aka gani da Bindiga Kirar AK-47

Yanzu-yanzu: Buhari ya bada umurnin a bindige duk wanda aka gani da Bindiga Kirar AK-47 Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bawa hukumomin tsaro umurnin bindige...

Ƙungiyar masu fataucin abinci zuwa kudancin ƙasar nan, Sun Amince Da Cigaba Da Kai kayan abinci Kudancin Nijeriya

Dillalan Abinci Sun Amince Da Cigaba Da Kai ka Ya Kudancin Nijeriya. Daga Comr Abba Sani Pantami Shugabannin dillalan Shanu da na Abinci a karkashin kungiyar...
%d bloggers like this: