Boko Haram sun zo mana da sabon Salo sun samu a tsaka mai wuya muna bukatar dauki GWAMNA MAI MALA BUNI.
_________

Gwamnan Yobe Mai Mala Buni ya ce suna cikin tsaka mai-wuya sakamakon hare-haren mayakan Boko Haram da suka tada musu hankali tun ranar Juma’ar makon da ya gabata.

Mai Mala ya ce sanin kowa ne halin da ake ciki a yankunan arewa maso gabashin Najeriya, sai dai hare-haren da suke gani a yanzu na tada hankula matuka kuma ya zama dole a tunkare su.

A tattaunawarsa da BBC, gwamna ya ce a baya komai ya yi sauki amma a wannan lokaci abin ya tsananta, saboda ba a san dalilan mayakan ba, kuma zuwansu na wannan lokaci ya sha bamban da wanda aka saba gani a baya. Domin sun zo da sabon salo.

A halin yanzu Daruruwan mutane sun tsere ne a gidajen saboda gudun kada a ritsa da su a musayar wutar da ake yi tsakanin sojojin Najeriya da mayaƙan Boko Haram, ko da yake akwai masu cewa da dama sun mutu.

Sai dai gwamnan ya shaida wa BBC cewa ba a zaune yake ba, a lokacin zantawar su da shi yana mai tabbatar da cewa yaje Abuja sun tattaunawa da hafsoshin tsaro a Abuja domin laluben mafita.

Ya ce, “Dama mayakan kan shigo jifa-jifa su wawushe kayan abinci da dukiya sai dai a wannan lokaci har kwana suka yi cikin garin. na giedam wanda basa haka a baya.

Mutanen garin sun shiga ɗimauta da yanayi na tashin hankali, wannan dalili ya tilasta musu tserewa domin neman mafaka a garuruwa makwabta.

Ina tattaunawa da babban hafsan tsaron Najeriya domin neman hanyoyin dakile mayakan, kuma yanzu haka garin ya dawo karkashin jami’an tsaro”, in ji Mai Mala Buni

Amma gwamnan ya nuna damuwarsa matuka inda yake cewa su a matakin jihar suna iya ƙoƙari domin ganin an samu saukin wannan al’amarin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here