Rundunar Sojojin Najeriya ta sha yin ikirarin cewa an yi galaba a kan ‘yan ta’addan kuma a lokuta da dama suna yin watsi da duk wani hasarar da aka yi.

Kungiyar ta’addanci ta yi sanadin mutuwar sama da 100,000 tare da raba miliyoyin mutane da muhallansu musamman a jihohin Adamawa, Borno da Yobe.

Mayakan kungiyar Boko Haram da ke samun goyon bayan kungiyar IS, ISWAP da a da ake kira Jamā’at Ahl as-Sunnah lid-Da’wah wa’l-Jihād sun kai farmaki kauyen Buratai da ke karamar hukumar Biu Karamar Hukumar Jihar Borno.

Buratai ne mahaifar tsohon babban hafsan soji, Yusuf Buratai.

SaharaReporters ta tattaro cewa ‘yan ta’addan sun afkawa al’ummar a safiyar Jiya litinin, inda suka rika harbi da manyan bindigogi.

Wata majiyar soji ta ce lamarin ya tilastawa mutane yin tattaki domin tsira da rayukansu da kuma kasancewa a cikin gida yayin da ake ci gaba da harbe-harbe.

“Yawancin mazauna garin sun gudu zuwa Miringa, wani gari a Biu. Ba zan iya cewa ko akwai wadanda suka jikkata ba, ”in ji shi.

Majiyar ta kara da cewa sojojin sun samu galaba a kan ‘yan ta’addan a wani artabu da suka yi da su, wanda hakan ya sa suka tsere.

Tun bayan rasuwar shugaban JAS, Abubakar Shekau, kungiyar ISWAP ke kara karfafa gwuiwa a yankunan da ke kusa da tafkin Chadi.

Kwanan nan, ta nada Wali Sani Shuwaram, mai shekaru 45 a matsayin sabon Shugaban (Wali) na ISWAP a tafkin Chadi.

Mambobin kungiyar sun kara yawaita biyo bayan sauya sheka na daruruwan mayakan Boko Haram karkashin Shekau.

Source: Daily True Hausa

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here