“Rashin gudanar da zaben kananan hukumomi, da nuna wariya a APCn Katsina ya sa na fice fit daga APC na koma PDP”
Sanata Babba Kaita
Sanata Ahmad Babba Kaita na shiyar Daura jihar Katsina ya bayyana jinkirin rashin yin zaben kananan hukumomin jihar Katsina kan lokaci, na daya daga cikin manyan dalilan da ya sa ya wagirar da jam’iyyar APC a jihar Katsina ya sauya sheka zuwa jam’iyyar PDP.
Sanata Kaita ya bayyana hakan ne a cikin wani dogon jawabin ficewarsa daga APC wanda mai taima wa sanatan a fannin yada labarai Malam Abdulkadir Lawal ya fitar da sanarwar a ranar Laraba kamar yadda Katsina Media Post News ta gani.
Haka kuma jawabin ya kara bayyana cewa yadda Gwamnatin APC ta Masari a Katsina take nuna wariya ga wasu jiga-jigan jam’iyyar, inda ta mayar da wasu a matsayin yayan bora, da kuma wasu ta mayar da su yayan mowa wannan ma ya kara tasiri matuka wajen dadin ficewar sanatan a cikin jam’iyyar.
Sannan Sanata Kaita ya nuna yadda aka yi babakere wajen zaben shuwagabannin jam’iyyar APC na jihar Katsina, da ba a yi wa bangarori da dama adalci ba, shima babban dalili ne a gare da ya nade tabarmasa daga cikin jam’iyyar APC, sannan magoya bayansa dama suka suna sha’awarsu na ya koma jam’iyya PDP, kuma tuni ya amsa kiransu.