NDLEA ta kama gidajen buredi da ke kwaba garin fulawa da ganyen Wiwi

Hukumar Hana Sha da Fataucin Muggan Kwayoyi (NDLEA) ta ƙama wasu gidajen Biredi dake kwaba fulawar yin buredi da ganyen Wiwi.

Wadannan gidaje sun hada da KNL Lounge dake hangar Lamingo da wanda ke Mining Quarters, Rantya Low Cost estate sannan da Tuscany Lounge dake hanyar Azaki Ave a cikin garin Jos.

Bugu da ‘kari majiyar Alfijir Hausa ta cigaba da shaida mana cewa; Daraktan yada labarai na hukumar Femi Babafemi ya sanar da haka ranar Litini a Abuja.

Muggan kwayoyin da hukumar ta kama sun hada kilogram 14 na Barcadin Codeine, kilogram 355.5 na Flunitrazapem, Exol-5, kilogram 30, Diazepam kilogram 2.5, Tramadol gram 370.1 da Pentazocine kilogram 1.5 a garin.

Shugaban hukumar NAFDAC dake jihar Filato Ibrahim Braji ya ce sun kama mutum biyar dake da hannu a safarar wadannan miyagun kwayoyi,

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here