Advert
Home Sashen Hausa BINCIKEN MUSAMMAN: ZABEN FITAR DA SHUGABA JAM'IYYAR APC NA TSAKA MAI...

BINCIKEN MUSAMMAN: ZABEN FITAR DA SHUGABA JAM’IYYAR APC NA TSAKA MAI WUYA !!!!

BINCIKEN MUSAMMAN:

ZABEN FITAR DA SHUGABA JAM’IYYAR APC NA TSAKA MAI WUYA !!!!

Daga Jaridun Katsina City News 13/10/2021

Duk wani dan jam’iyyar APC a Jihar Katsina, jininsa yana kan akaifa, sakamakon zullumin da yake ciki a kan me taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar da za a yi gobe Alhamis 14/10/2021 zai haifar?

A wannan taron ‘yar nune za ta nuna ina aka dosa. Za a faro yadda aka fara ne? Ko ko za a yi dan waken zagaye? A kan fitar da zaben shugabannin jam’iyyar na Jiha.

Ranar Asabar 16/10/2021 aka fitar a ranar da za a tabbatar da wanda aka zaba ya zama Shugaban jam’iyyar APC na Jihar Katsina.

Jini na hawa, gari yana kara daukar zafi a kan ‘yan takara biyu da yanzu sune sunansu ya yi fice.

Bala Abu Musawa, mataimakin Shugaban jam’iyyar APC daga yankin Funtua.

Alhaji Shitu S. Shittu, Shugaban jam’iyyar APC na Jihar Katsina har karo uku. Ya rike a matsayin riko sau biyu, an kuma zabe shi sau daya.

Bala Abu ya fito daga yankin Funtua, wanda tasirinsu a siyasar Katsina sune kan zama raba gardama wajen fito da dan takara a kowace jam’iyya tun da aka fara dimokaradiyya.

Yanzu suna magana da murya daya a kan zaben Shugaban jam’iyya shi ne suna son Bala Abu Musawa ya zama Shugaba.

Shittu S. Shittu ya fito daga shiyyar Katsina. Shiyya marar Tabbas ce a siyasa, ba kuma wanda ya isa ya ce shi ne ya mallake ta. Kananan Hukumomi 12 da suka fito a shiyyar, kowacce Karamar Hukuma akwai wani mai karfin da ke goyon bayan ta, kuma babu mai tabbas a kan shi.

A jadawalin siyasa, Shittu S. Shittu ba shi da iko gam-gam da shiyyar Katsina. Allura ce cikin ruwa, mai rabo ka dauka.

Shiyyar Daura ita kuma rarrabe take tsakanin Kananan Hukumomin masarautar Daura da ‘yan shiyyar Daura da kuma ‘yan Daura. Misali, Kankia, Kusada, Ingawa, wasu ke iko da su, haka Dutsi, Mashi da sauran su na wasu ne.

Shiyyar daura ita ma rarrabe take, kamar Burodi ne a gaban majiya yunwa, sai abin da ka yi sa’ar samu. Haka take a siyasance.

Jihar Katsina ta dau zafi, bisa tsammanin za a dankara wani dan takara a kan ‘yan jam’iyya ba za a bar su su zabi wanda ransu ke so ba.

Majiya mai karfi ta tabbatar mana cewa wasu ‘yan takara har sun mallaki fom na Shugaban jam’iyya suna jiran su ji za a yi masu rashin adalci? Su cika su shelanta tsayawa takara.

Wasu kuma sun shirya shirin jerin gwanon lumana kafin zaben in suka ga ana neman yin a-dankara.

“Bayan rantsuwa, za mu cika Katsina da magoya bayanmu, za mu yi taron manema labarai na duniya, za mu diga dan ba na yakar jam’iyyar ta ciki da waje, in muka ga kamshin rashin gaskiya”, in ji wani jigo, yana fada wa babban Editan jaridunmu.

Yanzu dai kallo ya koma sama, Shaho ya dauki Giwa. An shiga mako mafi tsawo ga ‘yan jam’iyyar APC.

Mu a jaridun Katsina City News, muna fatan za a wanye lafiya, bisa la’akari da mutuncin da Shugaban Kwamitin zabubbakan, Alhaji Muntari Lawal yake da shi da masu mara masa baya.

Sannan Gwamnan Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari, gogaggen dan siyasa ne, sakaina ce iya ruwa.

A karatun siyasa, shi Farfesa ne, ya san ta, ta san shi, ya kuma san hatsarin fusatar ‘yan siyasa, ba zai bari ta kai ga haka ba.

Katsina City News

www.katsinacitynews.com

Jaridar Taskar Labarai

www.jaridartaskarlabarai.com

The Links News

www.thelinksnews.com

07043777779 081377777245

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

Gwamnatin Katsina ta Amince da gina hanyar ƙarƙashin ƙasa (Underpass Road) a cikin Birnin katsina…

  A zamanta na yau Laraba 20 ga watan Oktoba 2021, Majalisar zartaswa ta jiha karkashin jagorancin Gwamna Aminu Bello Masari ta amince da gina...

PHOTOS: Buhari Receives Turkish President Erdogan, Wife in Abuja

The President, Major General Muhammadu Buhari (retd.), has received the Turkish President, Recep Tayyip Erdogan and his wife, Emine at the State House in...

Gwamnatin Kaduna ta ce an kashe mutum 343 cikin wata uku a jihar

Daga: Comrade Musa Garba Augie. Gwamnatin Jihar Kaduna ta tabbatar da mutuwar mutum 343 sakamakon ayyukan 'yan fashin daji da sauran tashe-tashen hankali cikin wata...

Shekarau ba uban Gidana bane A siyasa ,,,, Abokin Siyasa Tane Kawai ,, Cewar Musa Iliyasu Kwankwaso…

Ni Bana Adawar Cikin Gida Amma Duk layin Dayake Na Gaskiya Shinake bi Kuma Layina Shine Abdullahi Abbas,,, Cewar Musa iliyasu Kwankwaso, Saidai Yayi tsokaci...

RIKICI TSAKANIN MAHDI SHEHU DA GIDAN REDIYON VISION FM KADUNA!

  Musa Ibrahim daga Kaduna @Katsina City News Wani rikici ya barke tsakanin malam mahadi shehu shugaban rukunin kamfanonin dialogue da kuma gidan rediyon vision FM...
%d bloggers like this: