Sirrin Jar Hula ko kuma Jar dara a kasar Nijar.
Jar dara har ma da bakar, sun samo asali ne daga kabilun barebari wato Kanem da Borno
Masu mulki ko masu kudi suke sa jar dara a yankin na barebari, har ya kai ga ‘yan siyasar na sawa bayan mulkin mallaka.
Tasirin Hular ya karu wajejen 1990, yayin manyan ‘yan siyasar kasar suna sanyawa kamar su:
-Shugaba Tandja Mamadou
-Shugaba Mahamadou Issoufou
– Shugaba Mahamane Ousmane
-da sauransu ….
wanda dukkan su asalinsu yan gabacin kasar ne.
A kasar Nijar musaman ma a yanayin kasar jar dara tana nema ta zama ta ‘yan siyasa.