Daga Auwal Isah.

A karon farko, Makarantar hardar Alkur’ani mai tsarki ta ” Bin sa’id Tsangaya Model School ” da ke a unguwar Tudun ‘yan lihidda, Katsina, ta yi bikin saukar dalibai guda biyar da suka Mahaddace Alkur’ani mai girma.

Taron bikin saukar daliban wanda ya gudana a Makarartar a ranar lahadin nan 16 ga Janairun nan na 2022, ya samu halartar iyayen daliban maza da mata da kuma baki daga wurare daban-daban a cikin jihar ta katsina.

Tun farko da yake jawabi a wajen taron, shugaban Makarantar, Abdulhakim Sa’id, ya bayyana tarihin kafuwar Makarantar da irin nasararoin da ta samu, sannan da wasu ‘yan kalubale da ba a rasa in-da-can ba daga lokacin da aka kafamakarantar ya kawo yanzu, inda daga cikin nasararorin da suka samu har da bikin saukar daliban makarantar a karon farko, inda ya bayyana haka a matsayin wata babbar nasara.

A lokacin bikin yaye daliban, daliban da aka yi wa saukar sun gabatar da karatuttuka daya-bayan-daya a matsayin nuna irin ingancin hardar kur’anin da suka yi suka yi a bainar jama’a. Haka kuma sauran dalibai sun gabatar da Makaloli a kan fannonin ilimin addini daban-daban, musamman falalar karatun alkur’ani da hardar sa.

Daga cikin manyan bakin da suka halarci taron bikin saukar daliban akwai; shugaban Munazzamatul Fityanul Islam na jiha Malam Shu’aibu Gambarawa, da tsohon mai ba gwamna shawara kan harkokin Almajirai Malam Lawal Mani Gambarawa, Malam Husaini Kibiya da sauransu.

Daga bisani, Malam Husaini Kibiya ya jagoranci biyawa daliban Allunansu na sauka, sannan kuma ya gabatar da takaitaccen jawabi a kan muhimmancin karatun alkur’ani da yin haddar sa ya kuma kwadaitar tare da kawo kissoshi dangane da albarkar da ke cikin girmama Malamai.

Daga karshe an ba da shaidar kammala hardar ga daliban, sannan aka yi hotunan tarihi aka kima raba kayan walima aka sallami jama’a.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here